'Yan Bindiga Sun Fadi Makudan Kudin da Za a Biya Kafin Su Sako Daliban da Suka Sace a Kaduna

'Yan Bindiga Sun Fadi Makudan Kudin da Za a Biya Kafin Su Sako Daliban da Suka Sace a Kaduna

  • Ƴan bindigan da suka sace ɗalibai 287 a jihar Kaduna, sun aika da saƙon kuɗaɗen fansan da suke son a biya su
  • Bayan sun kira waya, miyagun sun nemi da biya su N1bn kafin su yarda, su bari ƴan makarantar su shaƙi iskar ƴanci
  • Sun kuma yi barazanar halaka yaran tare da malamansu idan har aka cika wa'adin kwanaki 20 ba tare da biyan kuɗaɗen ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Ƴan bindigan da suka sace ɗalibai 287 a wata makarantar gwamnati da ke Kuriga a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna sun buƙaci a biya su N1bn domin sako yaran.

Masu garkuwa da mutanen da suka sace ɗaliban sun bayyana buƙatarsu ne bayan sun tuntuɓi Aminu Kuriga, wani abokin shugaban makarantar, Abubakar Isah, a ranar Talata, a cewar rahoton jaridar Premium Times.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi kudin fansan da gwamnatinsa za ta biya don ceto daliban da aka sace a Kaduna

'Yan bindiga sun nemi kudin fansa
'Yan bindiga na son N1bn kafin sako daliban Kaduna Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Ƴan bindiga sun faɗi buƙatarsu

Wani mazaunin garin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana hakan, inda ya ƙara da cewa sun bada wa'adin kwanaki 20 domin a biya kuɗin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Ƴan ta’addan sun buƙaci a biya su N1bn bayan sun tuntuɓi wani abokin shugaban makarantar, Aminu Kuriga, da misalin ƙarfe 2:00 na rana a ranar Talata.
"Ɗaya daga cikin masu garkuwa da mutanen ya kira waya, ta hanyar ɓoye lambarsa. Ya ce suna can gefen arewacin Dansadau (wani ƙauye a ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara) idan muka kawo kuɗin za su saki yaran.
"Sun bada wa'adin kwanaki 20 daga ranar da suka sace ɗaliban domin biyan kuɗin fansan. Sun ce za su halaka yaran da malaman idan har ba a cika sharaɗinsu ba.

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Jaridar Daily Post ta ce har yanzu dai gwamnatin jihar Kaduna ba ta ce uffan ba kan lamarin. Sannan ba a samu jin ta bakin kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar ba, Samuel Aruwan.

Kara karanta wannan

Fasinjoji da dama sun bace yayin da 'yan bindiga suka farmaki wata mota a Taraba

Sai dai mai magana da yawun ƴan sandan jihar, ASP Mansir Hassan ya ce rundunar ba ta da masaniya kan wannan buƙatar ta ƴan bindigan.

Ya ce suna ci gaba da ƙoƙarin ganin an sako yaran ba tare da wani sharaɗi ba.

Ba batun biyan kuɗin fansa - Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Tinubu ta ce ba za ta biya kuɗin fansa ba kan ɗaliban da aka sace a Kaduna.

Gwamnatin ta ce ko sisi ba za ta biya ba, yayin da ta umurci jami'an tsaro da su gaggauta ceto ɗaliban daga hannun ƴam ta'addan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel