Gwamna Ya Yi Magana kan Jita Jitar Yi wa Wike Barazana a Taron Tinubu

Gwamna Ya Yi Magana kan Jita Jitar Yi wa Wike Barazana a Taron Tinubu

  • Gwamna Francis Nwifuru ya yi martani game da rahotannin da ake yaɗawa wai ya yi wa Nyesom Wike barazana
  • Nwifuru ya ce kalmar da gwamnan ya yi amfani da ita ishara ce ga hukunci kan masu yaɗa ƙarya, ba barazana ga Wike ba
  • Gwamnatin ta zargi ɓangarorin PDP da karkatar da kalaman gwamnan domin haddasa saɓani tsakaninsa da Wike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abakaliki, Ebonyi - Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru, ya yi karin haske game da rahoton cewa ya yi wa Nyesom Wike barazana.

Gwamna ya musanta zargin cewa ya yi wa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, barazana a taron goyon bayan Shugaba Bola Tinubu da sauran 'yan akarar APC.

Gwamna ya musanta yi wa Wike barazana a taron Tinubu
Gwamna Francis Nwifuru da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Rt. Hon. Francis Nwifuru, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na Ebonyi, Ikeuwa Omebe, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Segalink ya yi maganar da ka iya zama barazana ga takarar Peter Obi da Kwankwaso a 2027

Gwamna ya zargi PDP da yada karya

Gwamnatin Ebonyi ta bayyana cewa rahotannin da ke cewa tsohon gwamnan Rivers ya fuskanci barazana ƙarya ne, kuma an ƙirƙire su ne domin haddasa saɓani tsakaninsu.

Ya zargi ɓangarori biyu na jam'iyyar PDP da karkatar da kalaman da Gwamna Nwifuru ya yi a taron da aka gudanar ranar 15 ga Yuni, 2026, a filin Pa Ngele Oruta da ke Abakaliki.

Omebe ya ce gwamnan bai taɓa yin wata barazana ga Wike ba, duk da yadda wasu shugabannin PDP da kafafen yaɗa labarai suka fassara jawabinsa.

Ya ce kalaman gwamnan sun shafi wasu 'yan adawa da ake zargi da tayar da rikici a Ebonyi tare da yaɗa labaran ƙarya da farfaganda suna amfani da sunan Barrista Nyesom Wike.

A cewarsa, kalmar da gwamnan ya yi amfani da ita ishara ce kawai cewa masu aikata irin waɗannan abubuwa za su fuskanci hukunci bisa doka idan ba su daina ba.

Gwamna ya musanta cewa ya yi wa Wike barazana
Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi. Hoto: Rt. Hon. Francis Nwifuru.
Source: Facebook

Alakar da ke takanin Gwamna Nwifuru da Wike

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda Lawal ya tirje, ya yi magana kan sulhu da ƴan bindiga a Zamfara

Kwamishinan ya jaddada cewa Francis Nwifuru da Nyesom Wike suna da kyakkyawar dangantaka wadda ta ginu kan mutunta juna, saboda haka babu dalilin da gwamnan zai yi masa barazana.

Ya ce yunƙurin ɓangarorin PDP da wasu kafafen yaɗa labarai na karkatar da jawabin gwamnan domin haddasa rashin jituwa tsakanin shugabannin biyu bai dace ba.

A cewarsa, jam'iyyar PDP ba ta da wata barazana ga APC a Ebonyi kafin zaɓen shekarar 2027, domin al'ummar jihar suna goyon bayan gwamnatin Nwifuru.

Sanarwar ta ƙara da cewa duk wani yunƙurin haddasa saɓani tsakanin Gwamna Francis Nwifuru da Barrista Nyesom Wike ba zai yi nasara ba, cewar Punch.

Gwamna ya sassauta hukunci kan ma'aikata

Mun ba ku labarin cewa Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ya sassauta kan matakin da ya dauka na ladabtar da wasu daga cikin jami'an gwamnatinsa.

Francis Nwifuru ya dage dakatarwar da ya yi wa kwamishinoni 25 da wasu jami'an gwamnati kan kin halartar wani muhimmin taro.

Gwamnan ya umarce su da su dawo bakin aikinsu ba tare da bata wani lokaci ba domin dorawa daga inda suka tsaya wajen sauke nauyinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.