Sojoji Sun Yi Nasara a Samamen da Suka Kai Dajin Zamfara, Sun ceto Jarirai da Mata

Sojoji Sun Yi Nasara a Samamen da Suka Kai Dajin Zamfara, Sun ceto Jarirai da Mata

  • Akalla mutane bakwai da suka hada da jarirai biyu da mata biyar ne dakarun sojoji na rundunar Hadarin Daji suka kubutar a Zamfara
  • Kakakin rundunar, Suleiman Omale ya ce watanni biyu wadanda aka kubutar suka shafe a hannun masu garkuwa da mutane a dajin
  • Omale ya yi nuni da cewa 'yan bindiga a dajin Zamfar ana karbar wuta ta ko ina daga hannun sojoji, wanda ke tilasta su guduwa ko a kashe su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Zamfara - Rahotanni sun bayyana cewa dakarun soji na Hadarin Daji (OPHD) sun kubutar da mata biyar da jarirai biyu a dajin Kuyambana da ke Zamfara.

Jaridar The Cable ta ruwaito kakakin rundunar, Suleiman Omale ya ce 'yan bindiga ne suka yi garkuwa da wadanda dakarun suka kubutar a kauyen Kagara da ke jihar Neja.

Kara karanta wannan

Buga takardun bogi: Kotu ta dauki mataki kan tsohon shugaban bankin NIRSAL, Abdulhameed

Sojoji sun kubutar da mata da jarirai a dajin Zamfara
Sojoji na ci gaba da kara kaimi wajen kai wa 'yan bindiga farmaki a dajin Zamfara.Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Sojoji sun kai samame dajin Kuyambana

Omale ya ce dakarun OPHD sun kubutar da mutanen bayan kai samame a sansanonin 'yan bindigar, inda ya kara da cewa kwanaki 80 mutanen suka kwashe a hannun masu garkuwan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A wani samame da dakarun suka kai dajin Kuyambana da ke Zamfara, sun kubutar da mata biyar da jarirai biyu.
"An yi garkuwa da su ne a watan Janairu 2024 daga kauyen Marange da ke karamar hukumar Kagara, jihar Neja."

A cewar Omale, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

"An mika mutanen 7 ga hukuma" - Omale

Kakakin rundunar ya kuma shaida cewa sojoji na ci gaba da kai hare-hare kan 'yan ta'adda a dajin Zamfara, da nufin kakkabe su daga dajin baki daya.

Ya ce:

"Muna ci gaba da matsin lamba kan 'yan bindiga a dajin Zamfara, wannan ne ma dalilin da ya sa dakarun suka yi nasarar kubutar da mutanen daga hannun masu garkuwa."

Kara karanta wannan

Yayin da ake cikin wani hali, Tinubu ya bada umarnin bude iyakokin Najeriya, bayani sun fito

Omale ya ce rundunar ta mika wadanda ta kubutar zuwa ga hukumomin da abin ya shafa domin gaggauta mayar da su ga iyalansu.

Babban kwamandan rundunar ta 8 a makarantar sojoji ta Sokoto, Manjo Janar Godwin Matkut, ya jinjinawa kokarin dakarun sojojin a wannan aikin da suka yi.

Sojoji sun kashe mayakan IPOB/ESN

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa sojojin da ke ba da tsaro a jihar Imo sun kashe wasu tsagerun kasar Biafra da kuma mayakan kungiyar ESN.

A hannu daya kuma, sojojin da ke aiki a Arewa maso yamma, sun yi nasarar kubutar da mutane 15 daga hannun 'yan bindiga a dajin Zamfara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel