Masu Garkuwa Da Mutane
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun yi garkuwa da Rogers a kusa da gidansa da ke Rumuosi a Fatakwal da misalin karfe 9 na daren ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu.
Wasu bata gari sun yi karfin hali yayin da suka yiwa 'yan sanda a jihar Akwa Ibom lokacin da ƴan sandan suka kama wani mai suna Udo da ake nema ruwa a jallo.
Hukumar kiyaye hadura ta kasa ta bayyana tukin ganganci a matsayin dalilin da yahaddasa hadarin da yayi sanadiyar mutuwar mutane shida da jikkata 21 a jihar Ogun
Rahotanni sun nuna cewa wasu mahara sanye da kakin sojojin sun yi awon gaba da tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Ribas a 2023, Jackrich, sun kashe mutum biyu.
'Yan bindigan da suka yi garkuwa da daliban jami'ar tarayya da ke Wukari a jihar Taraba sun bukaci a ba su kudin fansa N50m kafin su bari su samu 'yanci.
Chief Elias Atabor, shugaban al'umar Agojeju-Odo da ke jihar Kogi, ya bayyana cewa adadin mutanensu da 'yan bindiga suka kashe ya karu zuwa 25 daga 19.
Da misalin karfe 1 na daren ranar Juma'a aka ruwaito wasu 'yan bindiga sun farmaki masu zuwa sallar Tahajjud a kauyen Kuta da ke Minna, babban birnin jihar Neja.
Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana illar da ƴan bindiga suka yi wa al'umma a ƙauyuka 551 da ke yankin ƙananan hukumomi 551, Uba Sani ya ware masu tallafi.
Dakarun hukumomin tsaro na hadin guiwa a jihar Anambra sun yi nasarar kashe ƴan bindiga huɗu yayin da ɗan sanda ɗaya ya mutu a wani musayar wuta.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari