Jami'an Tsaro Sun Yi Ƙazamin Artabu da Ƴan Bindiga, Mutane da Yawa Sun Mutu

Jami'an Tsaro Sun Yi Ƙazamin Artabu da Ƴan Bindiga, Mutane da Yawa Sun Mutu

  • Jami'an tsaro sun kai samame maɓoyar ƴan bindiga guda biyu, sun yi kazamin artabu a jihar Anambra da ke Kudu maso Gabas
  • Rahotanni sun bayyana cewa an kashe ƴan bindiga 4, ɗan sanda ɗaya yayin da wasu da dama suka ji raunuka a musayar wutar
  • Rundunar ƴan sanda ta ce dakarunta sun kara faɗaɗa farautar ƴan bindigar zuwa yankuna da dama domin kamo su

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Anambra - Akalla mutane biyar ne ake fargabar sun mutu wasu kuma sun jikkata a wani artabu da aka yi tsakanin jami’an tsaro da ‘yan bindiga ranar Talata a Anambra.

Lamarin ya faru ne a lokacin da jami’an tsaro na hadin gwiwa na jihar Anambra (JSF) suka kai hari sansanoni biyu na ‘yan bindigar, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sanya mutane farin ciki awanni 24 bayan sace kananan yara 30 a Arewa

Jami'an yan sanda.
An kashe yan bindiga 4 da ɗan sanda a Anambra Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Getty Images

Sansanonin ƴan bindiga da jami'an tsaron suka kai samame sun haɗa da wanda ke a Ogboji, karamar hukumar Orumba ta Kudu da Aguluezechukwu a ƙaramar hukumar Aguata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'ai sun kwato kayayyaki

A yayin samamen da jami’an tsaro suka kai, sun kwato wasu kayayyaki kamar na’urar harba roka da aka yi a cikin gida, laya, kakin ‘yan sanda da dai sauransu.

Duk da har yanzun jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Anambara, Ikenga Tochukwu, bai faɗi adadin waɗanda suka mutu ba amma bayanai sun nuna an rasa rayuka 5.

An kashe wasu yan bindiga 4

Rahoton da Punch ta tattaro ya nuna cewa ƴan bindiga huɗu da ɗan sanda guda sun rasa rayuwarsu a musayar wutar da aka yi.

Wata majiya ta ce yankin ya koma tamkar filin yaki a lokacin artabun yayin da harsasai ke ta yawo da ƙara, lamarin da ya sa mazauna yankin tsoro da fargaba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai sabon farmaki a jami'ar Arewa, sace dalibai

Wata sanarwa da rundunar ‘yan sanda ta fitar a Awka a ranar Laraba, ta nuna cewa dakaru sun faɗaɗa farautar ‘yan bindigar zuwa dajin Obofia, Aguluezechukwu da kuma Ogboji.

An sako yaran da aka sace a Katsina

A wani rahoton na daban Ƙananan yara 30 da ƴan bindiga suka sace a kauyen Kasai da ke yankin ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina sun shaƙi iskar ƴanci.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Katsina, ASP Abubakar Sadiq, ya ce masu ruwa da tsaki a yankin sun taimaka wajen ceto yaran.

Asali: Legit.ng

Online view pixel