Neja: ’Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masu Ibada a Lokacin Sallar Tahajjud

Neja: ’Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masu Ibada a Lokacin Sallar Tahajjud

  • Rahotanni sun bayyana cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari kan masu ibada a lokacin sallar Tahajjud a wani kauyen Minna, jihar Neja.
  • Mazauna yankin sun shaida wa manema labarai cewa 'yan bindigar sun kai farmaki da karfe 1 na dare lokacin da za a fara sallar dare
  • A cewar wani Aliyu Isah, akwai mazauna garin da ke hannun 'yan bindigar kusan kwanaki biyar kenan ba a sako ba, yanzu sake dawowa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Minna, jihar Neja - A daren ranar Juma'a ne wasu mahara suka tare hanyar Kuta da ke Minna babban birnin jihar Neja, inda suka far wa mutanen da ke zuwa sallar Tahajjud.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun ƙara shiga Abuja, sun tafka mummunar ɓarna a watan azumi

'Yan bindiga sun kai wa Musulmai hari a jihar Neja
'Yan bindigar sun kai farmakin a lokacin da Musulmi ke hanyar zuwa Tahajjud. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

'Yan bindiga sun tare masallata

Mazauna yankin sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 1 na dare a lokacin da Musulamai ke fitowa yin sallar Tahajjud.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daya daga cikin mazauna garin, Aliyu Isah, ya ce ‘yan bindiga dauke da mugayen makamai sun yi garkuwa da mazauna garin Minna tsawon kwanaki biyar da suka gabata.

Ya ce yankunan da suka fi kai wa farmaki sun hada da Kpakungu, Soje, Anguwan Daji, Limawa, Ogbomosho da dai sauransu.

'Yan sanda sun dauki mataki

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Vanguard, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce ‘yan sanda na kan gaba a lamarin.

“Rundunar ‘yan sanda na sintiri a kodayaushe suka samu rahoton bullar 'yan bindigar, kuma ana kama su a duk inda abin ya faru."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shiga masallaci sun dauke masallata ana sallar dare a Jihar Arewa

- Wasiu Abiodun

Zamfara: An sace masu sallar Tahajjud

A wani labarin makamancin wannan, Legit Hausa ta ruwaito cewa wasu 'yan bindiga sun shiga har cikin masallaci sun sace masallata a jihar Zamfara.

Rahotanni sun bayyana cewa nasallatan na sallar Tahajjud ne a lokacin da 'yan bindigar suka farmake su, inda har wasu suka jikkata.

Tun bayan shigowar watan Ramadan, an samu rahotanni da dama na kai hare-hare kan masu ibada a jihohin Arewa, musamman a kwanaki goma na karshe da ake fita sallar Tahajjud.

Asali: Legit.ng

Online view pixel