Daliban Jami’ar Tarayya Ta Gusau da Aka Sace Sun Samu ’Yanci

Daliban Jami’ar Tarayya Ta Gusau da Aka Sace Sun Samu ’Yanci

  • Ragowar daliban jam'iar gwamnatin tarayya dake Gusau sun samu 'yanci bayan shafe watanni a hannun masu garkuwa da mutane
  • Cikin wadanda aka samu nasarar cetowa har da masu hidimar kasa da aka sace a jihar Sokoto a watannin baya
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa an samu kubutar da su ne a yankin Kuncin Kalgo dake karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Ragowar daliban jami’ar tarayya da ke Gusau, Jihar Zamfara da aka sace a ranar 22 ga Satumba, 2023, sun samu ‘yanci.

In baku manta ba dai wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki gidajen kwanar dalibai a unguwar Sabon-Gida da ke karamar hukumar Bungudu a jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da dalibai sama da 20, wadanda yawancinsu mata ne.

Kara karanta wannan

Gurfanar da Ganduje da iyalansa a gaban kotu, halin da ake ciki a jihar Kano

Dauda Lawal
An sace daliban ne tin 22 ga watan Satumba, 2023 a karamar hukumar Bungudu. Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Bayan kokarin da hukumomin jami'ar da 'yan uwa suka yi, an sako wasu daga cikin wadanda aka kama bayan watanni, amma 23 sun ci gaba da kasancewa a hannunsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai an ruwaito cewa jami’an tsaro sun ceto sauran daliban a ranar Lahadin da ta gabata, cewar jaridar Aminiya.

In da aka samo daliban

Rahoton ya tabbatar da cewa an sako su ne su 23 a Kuncin Kalgo da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara kuma aka mika su ga jami’an gwamnati ranar Lahadi.

Jaridar Daily Trust ta tabbatar da cewa ta ga hotunan wasu da aka yi garkuwa da su a cikin motocin bas.

Majiyar ta kara da cewa an kubutar da wasu daga cikin masu yi wa kasa hidima da aka sace a jihar Sokoto.

Halin da jihar Zamfara ke ciki

Kara karanta wannan

Fusatattun Yarbawa na son a raba Najeriya, sun farmaki sakateriyar gwamnati a Oyo

Jihar Zamfara dai na daya daga cikin jihohin da rikicin masu garkuwa da mutane ya shafa a yankin Arewa maso Yamma.

A lokacin da ya nemi ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu a watan da ya gabata, gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya ce 'yan ta'adda sunyi wa jiharsa kawanya. Ga abinda yake cewa:

“An kai hare-hare da dama a wasu kananan hukumomin. Ina jin a matsayina na gwamna, ya kamata in sanar da yanayin ga mai girma shugaban kasa, wanda ya nuna jin dadin tattaunawar da muka yi, kuma muna neman karin jami’an soji da kuma kayan aikin da za su yi aiki yadda ya kamata da kuma kula da yanayin tsaron jihar."

-Dauda Lawal, gwamnan jihar Zamfara

An sace dalibai a jihar Zamfara

A wani rahoton kuma kunji cewa, an shiga cikin tashin hankali yayin da 'yan bindiga su ka kai farmaki Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau.

Maharan sun kai farmakin ne da misalin karfe 3 na dare dakunan dalibai uku tare da sace dukkan daliban da ke dakunan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel