'Yan Bindigan da Suka Sace Dalibai a Arewa Sun Bayyana Kudin Fansan da Za a Ba Su

'Yan Bindigan da Suka Sace Dalibai a Arewa Sun Bayyana Kudin Fansan da Za a Ba Su

  • Ƴan bindigan da suka yi garkuwa da ɗaliban jami'ar tarayya da ke Wukari sun bayyana kuɗin fansan da za a ba su
  • Tsagerun sun buƙaci a ba su Naira miliyan 50 kafin su sako ɗaliban waɗanda suka sace a ɗakunan kwanan ɗalibai da ke wajen makarantar
  • Jami'an tsaro dai na ci gaba da bada himma wajen ganin sun ceto ɗaliban cikin ƙoshin lafiya ba tare da sun cutu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - Ƴan bindigan da suka sace ɗalibai biyu na jami’ar tarayya da ke Wukari a jihar Taraba sun buƙaci a biya su kuɗin fansa fansa Naira miliyan 50.

Shugaban sashen yaɗa labarai na jami'ar, Ashu Agbu, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta wayar tarho, cewar rahoton tashar channels.

Kara karanta wannan

Karin kudin lantarki: Sanatan APC ya soki gwamnatin Bola Tinubu

'Yan bindiga sun bukaci kudin fansa
'Yan bindiga sun bukaci a ba su N50m kafin su sako daliban da suka sace Hoto: @Agbukefas
Asali: Twitter

Kimanin kaso 90% cikin 100% na dalibai da ma’aikatan jami'ar suna zaune ne a wajen harabar makarantar kamar yadda mataimakin shugaban jami’ar ya bayyana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka sace ɗaliban

Ƴan bindigan sun kai hari ne a shagon da ke jikin ɗaya daga cikin rukunin ɗakunan kwanan ɗaliban a ranar Laraba, 3 ga watan Afirilun 2024, inda suka ɗauke ɗalibai biyu da suke aiki a matsayin ma'aikata a wajen.

Ɗaliban sun dawo rubuta jarabawa ne saboda faɗuwar da suka yi lokacin da tsautsayin ya ritsa da su.

A cewar Agbu, ƴan bindigan sun bayyana cewa sun zo ne domin su ɗauke mamallakin shagon ba ma'aikatansa ba kuma za su dawo domin yin awon gaba da shi.

Ta bayyana cewa jami'an tsaro da matasa suna ci gaba da bin sahun ƴan bindigan kuma ba za su saurara ba har sai sun ceto ɗaliban cikin ƙoshin lafiya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutum 19 a wani sabon hari a jihar Arewa

Sojoji sun fatattaki ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji na bataliya ta 114 na sojojin Najeriya tare da haɗin gwiwar wasu jami’an tsaro a ranar Asabar sun tarwatsa maboyar ƴan bindiga a jihar Taraba.

Dakarun sojojin sun kuma kuɓutar da wasu mutum huɗu da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Yorro ta jihar Taraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel