'Yan bindiga Sun Saki Daliban Taraba Bayan Biyan Makudan Kuɗin Fansa

'Yan bindiga Sun Saki Daliban Taraba Bayan Biyan Makudan Kuɗin Fansa

  • Ɗaliban jami'ar Wukari, Joshua Sardauna da Elizabeth Obi sun shaƙi iskar ƴanci bayan shafe mako biyu a hannun ƴan bindiga
  • Shugabar sashen hulɗa da jama'a ta jami'ar, Ashu Agbu ta tabbatar da cewa ɗaliban suna tare da ƴan uwansu
  • Ƴan bindigar sun nemi a biya fansar miliyan ₦50 amma aka yi ciniki zuwa miliyan ₦20, daga bisani aka biya dubu ₦700 kowannensu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Taraba- Ɗaliban jami'ar tarraya ta Wukari da ke jihar Taraba sun shaƙi iskar ƴanci bayan shafe aƙalla mako biyu a hannun ƴan bindiga.

TVC News ta ruwaito cewa an saki ɗaliban ne bayan kowannensu ya biya wani kayyadadden adadi na kuɗin fansa.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya sun ƙi amincewa da biyan harajin ₦3000 domin hawa babban titin Legas-Calabar

Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ko wani jami'in dan sanda bai ce komai kan sakin daliban ba
Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ko wani jami'in dan sanda bai ce komai kan sakin daliban ba Hoto: @GovAgbuKefas
Asali: Twitter

Jami'ar hulda da jama'a ta jami'ar, Ashu Agbu ta tabbatarwa manema labarai sakin ɗaliban, inda rahotanni suka ce an sake su ne a ƙauyen Chinkai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An biya ₦1.4m a matsayin kuɗin fansa

Rahoton Daily Trust ya ce daliban sun samu kuɓuta bayan ƴan uwan kowanne ɗalibi sun biya ₦700,000 a matsayin kuɗin fansa ga ƴan bindigar. Jumilla an biya ₦1.4m kafin samun damar ceto daliban biyu.

Tun da fari, rahotanni sun ce ƴan bindigar sun buƙaci a biya su Naira miliyan 50 daga baya ciniki ya sauko zuwa Naira miliyan 20.

Amma daga baya ƴan bindigar suka karɓi Naira miliyan 1.4 kafin suka sako Joshua Sardauna da Elizabeth Obi a daren Alhamis.

Zuwa wannan lokaci babu cikakken bayanin halin da ɗaliban suke ciki, kuma rundunar ƴan sanda ba ta ce komai kan lamarin ba.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali bayan jami'an NSCDC sun harbi wata mata a filin Idi

An shiga fargaba bayan sace ɗalibai

A ranar 3 ga watan Afrilu, 2024 ne wasu tsagerun ƴan bindiga suka kai farmaki jami'ar tarayya ta Wukari dake jihar Taraba.

A wannan harin ne suka ɗauke ɗaliban biyu da ke aiki a rukunin shaguna dake jikin ɗakin kwanan ɗaliban jami'ar.

Joshua Sardauna da Elizabeth Obi na a matsayin ma'aikata a wasu daga cikin shagunan da maharan suka kaiwa farmaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel