Miyagun Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum 2, Sun Yi Garkuwa da Ɗan Takarar Gwamna

Miyagun Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum 2, Sun Yi Garkuwa da Ɗan Takarar Gwamna

  • Wasu ƴan bindiga sun kai farmaki gidan ɗan takarar gwamna a jihar Ribas kuma sun yi awon gaba da shi zuwa wurin da ba a sani ba
  • Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigar sun sace Sobomabo Jackrich tare da kashe mutum biyu da suka taras tare da ɗan siyasar
  • Rundunar ƴan sandan reshen jihar Ribas ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta faɗi wasu muhimman bayanai kan abin da ya auku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Wasu miyagun ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗan takarar gwamnan jihar Ribas karkashin inuwar jam'iyyar NRM a zaɓen 2023, Sobomabo Jackrich.

Sabomabo Jackrich.
An yi garkuwa da ɗan takarar gwamna a Ribas Hoto: Amb Sabomabo Jackrich
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar Punch ta tattaro, maharan sun yi awon gaba da ɗan siyasar yayin da suka kai farmaki har cikin gidansa a Usokun da ke ƙaramar hukumar Degema.

Kara karanta wannan

InnalilLahi: Ƴan bindiga sun halaka jami'an tsaro 30 ana shirin ƙaramar sallah a Arewa

An tattaro cewa ƴan bindigar na sanye da kakin sojoji yayin da suka sace Mista Jackrich ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu. 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan kuma bayanai sun nuna cewa maharan sun kashe mutum biyu, magoya bayan tsohon ɗan takarar gwamnan, waɗanda suka tarar a tare da shi.

Bayan kashe mutanen biyu, ƴan bindiga sun kwashi gawarwakin sun tafi da su tare da Mista Jackrich.

Wanene Jackrich da aka yi garkuwa da shi?

Jackrich, wanda aka fi sani da ‘Egberipapa’ yana ɗaya daga cikin tsofaffin tsagerun Neja Delta wanda suka rungumi shirin afuwa a zamanin marigayi shugaban kasa, Umar Yar’Adua.

Da yake mayar da martani kan lamarin, mai magana da yawun Mista Jackrich, Soibibo Sokari, ya tabbatar da kashe mutum buyu da kuma sace mai gidansa.

Sai dai wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce wasu dakarun sojoji ne suka yi awon gaba da tsohon shugaban tsagerun, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki kan dan majalisa har cikin gida a jihar Arewa

Yan sanda sun tabbatar da lamarin

Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sandan jihar Ribas, Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da aukuwar lamarin amma ta ce ba garkuwa da ɗan siyasar aka yi ba.

"Ba garkuwa da shi aka yi ba, yana tare da wasu jami'an tsaro, abin da zan iya cewa kenan a yanzu," in ji ta.

Emefiele ya koma hannun EFCC

A wani rahoton kuma kotu ta ba da umarnin cewa hukumar EFCC ta tsare tsohon gwamnan babban bankin Najeriya a hannunta.

Wannan umarni na zuwa ne bayan Godwin Emefiele ya sake gurfana a gaba babbar kotun jihar Legas kan wasu tuhume-tuhume 26.

Asali: Legit.ng

Online view pixel