Abubuwa 4 da Tinubu Ya Kamata Ya Yi Domin Tabbatar da Tsaron Makarantu a Najeriya, Kungiya

Abubuwa 4 da Tinubu Ya Kamata Ya Yi Domin Tabbatar da Tsaron Makarantu a Najeriya, Kungiya

  • Kungiyar ImpactHouse ta ce yawaitar garkuwa da dalibai a fadin Najeriya ya nuna muhimmancin daukar matakai na kare makarantu
  • John Andah, babban darakta na kungiyar, ya nemi gwamnatin Tinubu da ta dauki matakai wajen tabbatar da tsaro a makarantun kasar nan
  • A wata sanarwa da Legit.ng ta samu, ImpactHouse ta bayyana matakai hudu da ya kamata Tinubu ta dauka domin tsaron makarantu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

FCT, Abuja - Kungiyar ImpactHouse Center for Development Communication, ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya tabbatar da ingantaccen tsaro da ingantaccen ilimi a Najeriya.

Kungiya ta ba gwamnati shawarar hanyar kare makarantu
'Yan Najeriya na jumamin shekaru 10 da sace 'yan matan Chibok da Boko Haram suka yi a shekarar 2014. Hoto: Anadolu, Picture Alliance
Asali: Getty Images

"Dalibai na karatu a cikin tsoro" - Andah

A bikin cika shekaru 10 da sace ‘yan matan Chibok a ranar Litinin, 15 ga Afrilu, ImpactHouse ta roki Tinubu da ya magance matsalar rashin tsaro, musamman a makarantu.

Kara karanta wannan

Rudin soyayya: Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da jami'inta ya kashe mace mai ciki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta koka da yadda yawancin dalibai a yanzu suna karatu a cikin yanayi na tsoro da rashin tabbas, wanda ke haifar musu da rauni a kwakwalwa.

John Andah, babban darakta na ImpactHouse, a sanarwar kungiyar a shafinta na Twitter ya zayyana matakan da ya kamata gwamnatin Tinubu ta dauka da suka hada da:

1. Tsare-tsaren gwamnati kan tsaro

Aiwatar da manufofin gwamnati kan tsaro, lafiya, da samar da makarantu marasa tashe-tashen hankula domin tabbatar da tsaron makarantu da ɗalibai.

2. Matakan tsaro a makarantu

Aiwatar da ingantattun matakan tsaro a makarantu domin dakile hare-hare da kuma tabbatar da saurin mayar da martani ga dukkanin wata barazana.

3. Tattara bayanan sirri

Haɗin kai da hukumomin tsaro wadanda abin ya shafa wajen tattara bayanan sirri kan yuwuwar wata barazanar tsaro ga makarantu tare da magance su da gaggawa.

Kara karanta wannan

Zamfara: Rashin tsaro ya zo ƙarshe bayan Tinubu ya ba da umarni, ya yi kus-kus da gwamna

4 Hukunta masu kai hare-hare

Tabbatar da cewa an gaggauta gurfanar da daidaikun mutane ko kungiyoyin da ke da alhakin kai hare-hare a makarantu a gaban shari'a tare da daukar matakan tabbatar da sun fuskanci hukunci.

Farashin kayayyaki ya fara sauka

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa farashin kayan abinci da na masarufi sun fara sauka a kasuwannin Najeriya sakamakon darajar da Naira ke samu a kasuwar hada-hada.

Rahoton mujallar Bloomberg ya nuna cewa tattalin arzikin Najeriya zai habaka yayin da farashin kayayyaki zai ci gaba da faduwa idan Naira ta ci gaba da yin daraja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel