Wasu Bata Gari Sun Lakadawa Jami'an 'Yan Sanda Dukan Tsiya

Wasu Bata Gari Sun Lakadawa Jami'an 'Yan Sanda Dukan Tsiya

  • Wasu bata gari sun yiwa 'yan sanda duka a jihar Akwa Ibom lokacin da ƴan sandan suka kama wani mai suna Udo da ake nema ruwa a jallo
  • Hukumar 'yan sanda ta tabbatar da cewa 'yan sandan da aka yiwa dukan suna kwance a asibiti suna karban magani
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar ya bayyana matakan da zasu dauka akan wanda suka aikata laifin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum

Jihar Akwa Ibom - An shiga wani irin yanayi bayan wasu bata gari sun Lakadawa jami'an 'yan sanda duk a jihar Akwa Ibom.

Lamarin ya faru ne a lokacin da ƴan sandan ke neman wani shugaban kungiyar asiri ruwa a jallo mai suna Udo a karamar hukumar Abak ta jihar.

Kara karanta wannan

Wuraren shakatawa 5 da ya kamata ku ziyarta yayin bukukuwan Sallah a Kaduna

Police IG
Kwamishinan yanda ya tura tawaga mai karfi domin sake kamo bata garin. Hoto NIgerian Police Force Facebook
Asali: Facebook

Jami’an da suka je kama Udo sunyi amfani ne motar gida da farin kaya. Bayan sun yi nasarar kama shi suna kan hanyarsu ta komawa, sai motarsu ta samu matsala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ne ya sa wanda ake nema ruwa a jallon ya yi karyar cewa masu garkuwa da mutane ne suka kama shi.

Al’amarin ya jawo hankalin matasan yankin kuma suka yi gangami suka kubutar da shi.

Bayan sun kubutar da shi sannan suka juya suka far wa jami’an biyu da adduna da sauran muggan makamai.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa lokacin da aka far wa ƴan sandan, sun nuna katin shaidar aiki amma hakan bai yi amfani ba.

Halin da 'yan sandan ke ciki

Ƴan sandan guda biyu da suka tsallake rijiya ta baya yanzu haka suna kwance a asibiti saboda dukan kawo wuka da suka sha.

Kara karanta wannan

Mutane 2 sun fada kogin Legas bayan mummunan hatsarin mota

Da ta ke tabbatar da faruwar lamarin, hukumar ‘yan sandan ta ce jami’an da abin ya shafa na karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba.

Kuma sun sha alwashin cewa ba za suyi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da kama wadanda suka aikata aika-aikan.

Za'a sake kamo Udo

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Waheed Ayilara ya umarci wata babbar tawagar bincike da ta hada kai da sauran jami’an tsaro domin sake cafke mai laifin da ake nema ruwa a jallon.

Sannan ya umurci rundunar da ta hada da sauran masu hannu a harin domin fuskantar hukuncin da ya dace.

An kai hari ofishin ƴan sanda

A wani rahoton kuma, 'yan bindiga sun kashe ɗan sanda ɗaya yayin da suka kai hari caji ofis a wani ƙauyen karamar hukumar Batsari a Katsina.

Rahoto ya nuna cewa maharan sun yaudari jami'an yan sandan ta hanyar sanya Hijabi sannan suka far musu kafin aka yi musayar wuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel