Manyan Labarai A Yau
Tsohon gwamnan jihar Edo, Sanata Adams Oshiomhole ya musanta rahotanni da ke nuna cewa ya yi zargin an yi sa hannun sanatoci na bogi a rahoton dakatar da Natasha.
Gwamnatin kasar Equatorial Guinea ta yi murabus. Mataimakin shugaban kasar ya sanar da cewa gwamnatin ta yi murabus kan rashin yin abin a zo a gani.
Jam'iyyar NDC ta kafa sharadin rantsuwa ga kowane dan takara ban da Peter Obi da Kwankwaso, ta ce ba za ta bari a rika sauya sheka ba kujerunta ba.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa a shirye yake ya sadaukar da ransa domin ceto daliban da 'yan bindiga suka yi awon gaba da su zuwa daji.
'Yan bindiga dauke da makamai sun tare wani basarake a kan hanya a jihar Plateau. Hatsabiban 'yan bindigan sun hallaka shi har lahira sakamakon harin.
Kotun daukaka kara da ke Abuja ta dakatar da hukumar INEC daga aiwatar da hukuncin da ya umarci soke rajistar ADC da wasu jam’iyyun siyasa biyar.
Jam'iyyar APC reshen jihar Gombe ta sake jaddada cewa har yanzu tsohon Ministan sufuri, Farfesa Isa Ali Pantami, mamba ne a cikinta. Ta ce bai yi murabus ba.
Akalla 'yan sanda uku aka tabbatar da sun rasa rayukansu yayin da motar sulke ta taka bam da ake zargin yan ta'adda ne suka dasa a jihar Zamfara.
Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya zama dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar ADC a zaben 2027. A baya ya nina baya son zama hakan.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari