Manyan Labarai A Yau
Matatar man Dangote da ke Legas ta sanar da rage farashin man fetur biyo bayan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Amurka da Iran don kawo karshen yaki.
Rundunar yan sanda reashen jihar Legas ta tabbatar da mutuwar mataimakin kwamishina, Khan Salihu, an ce ya koma gida bayan fitowa daga masallaci ranar Lahadi.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC a zaben shekarar 2027, Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan hukuncin da kotu ta ba da na soke rajistar jam'iyyar ADC.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da shirin gudanar da auren gata. Gwamnan ya ware N1.5bn domin aurar da dubunnan mutane a jihar Kano.
Dan takarar gwamnam jihar Kano a karkashin inuwar jam'iyyar NDC, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya zabi yaron Kwankwaso a matsayin abokin takararsa a 2027.
An samu rahoton rasuwar daya daga cikin Alhazan Najeriya da ke kasa mai tsarki. Alhajin ya rasu ne bayan ya gamu da hatsarin mota a birnin Makkah.
Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Fansan Yamma sun samu nasara kan 'yan ta'adda a jihar Borno. Sojojin sun hallaka masu yawa bayan kai hari.
Manjo Janar Rabe Abubakar ya mutu ne a hannun 'yan bindiga bayan fiye d kwanaki 10 da sace shi a Katsina, tuni aka dauko gawarsa aka birne shi a Katsina.
Tsohon mai magana da yawun hedkwatar tsaro ta kasa, Manjo Janar Rabe Abubakar, ya rasu a hannun 'yan bindiga kamar yadda gwamnatin jihar Katsina ta sanar.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari