Manyan Labarai A Yau
Kungiyar Kiristoci ta CCCN ta zargi jam’iyyar APC da tara gayyar malaman addini na bogi,a wajen gabatar da 'dan takarar mataimakin shugaban kasa, Shettima.
Hukumar da ke kula da shige da ficen jiragen sama ta Najeriya ta dakatar da lasisin kamfanin jiragen sama na Dana Airlines har sai baba ta gani daga Laraba.
NDLEA ta gabatar da hujjojin kwayoyi da Daloli a shari'ar Abba Kyari. Hukumar NDLEA ta kira mutum uku da ya bada shaida a kotu a shari’ar ta da su Abba Kyari.
Majalisar dattawa a ranar Laraba, 20 ga watan Yuli, ta tabbatar da Mista Joe Ohiani a matsayin shugaban hukumar Hukumar Kula da Ayyukan More Rayuwa ta ICRC.
Dakarun Operations Hadin Kai, sun tabbatar da ceto wata yar makarantar Chibok, Ruth Bitrus, wacce ta kubuta daga hannun yan ta'addan Boko Haram tare da danta.
Dan mai martaba tsohon sarkin Kano, Mustapha Lamido Sanusi, ya kammala karatunsainda ya samu digiri mafi daraja a bangaren tattalin arziki a jami’ar Birtaniya.
Yan sanda sun kama wani matashi, Umar Sani, sun gurfanar da shi kan zargin satar injin janareto da lasifikan wani Masallaci a Yola, babban birnin jihar Adamawa.
Gwamnatin tarayya ta hararo hadarin tsadar da kayan abinci suka yi a yau. Minista ya ce tsadar abinci zai kara jefa mutane a talauci idan ba a dauki mataki ba.
Kwanaki kungiyar Kano First Forum ta nemi a hana Gwamna Abdullahi Umar Ganduje cin bashi. A jiya Alkali ya halattawa Gwamnatin Ganduje karbo danyen bashin.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari