Ido Zai Raina Fata, Mun ba Shugaban Kasa Rahoton Fasa Gidan Yarin Kuje inji Minista

Ido Zai Raina Fata, Mun ba Shugaban Kasa Rahoton Fasa Gidan Yarin Kuje inji Minista

  • Rahoton farko na bayanin yadda ‘Yan ta’adda suka fasa gidan yarin Kuje ya isa fadar Shugaban kasa
  • Ministan harkokin cikin gida na kasa ya tabbatar da cewa za a hukunta duk wanda aka samu da laifi
  • Rauf Aregbesola ya tabbatar da cewa jami’an leken asiri sun samu labarin ana shirin kawo wannan harin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - An soma gabatarwa Mai girma shugaban kasa da somin-tabin rahoton harin da ‘yan ta’adda suka kai a gidan gyaran hali da ke Kuje, garin Abuja.

Premium Times ta ce Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ya shaida mata wannan.

Da yake bayani a ranar Alhamis, 21 ga watan Yuli 2022, Rauf Aregbesola ya ce an tattara sunayen masu laifi da wadanda suka yi sakaci, har aka kai harin.

Kamar yadda Mai girma Ministan ya shaidawa manema labarai a karshen makon nan, gwamnati za ta dauki mataki na hukunta wadanda aka samu da laifi.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Sake Kama Wasu Da Suka Tsere Daga Kurkukun Kuje A Jihohin Arewa 2

“An aikawa shugaban kasa gajeren rahoto a game da abin da ya faru a gidan gyaran hali na Kuje. Nan gaba za a fitar da cikakken rahoto a karshen binciken.”
“Mun gano duk wadanda aikinsu ko sakacinsu ya yi sanadiyyar da aka yi wannan abin takaici, kuma duk wanda aka samu da laifi, za su dandana kudarsa.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gidan yari
Bayan kai hari a Gidan yarin Kuje Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Akwai laifin jami'an tsaro

Jaridar ta rahoto Ministan yana mai cewa jami’an da ke tattara bayanan sirri sun yi kokarin hana a kai hari a gidan kurkukun, amma jami’an tsaro suka yi sake.

Bayanin na Aregbesola ya tabbatar da zargin da ake yi na cewa jami’an leken asiri sun ankarar da sojoji da ‘yan sanda cewa ‘yan ta’adda na yunkurin kawo hari.

Duk da jan-kunnen da aka yi, a karshe mutane 800 suka sulale daga gidan yarin a tsakiyar Abuja. Daga ciki akwai mutum 60 da ake zargin ‘Yan Boko Haram ne.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Gwamnatin Buhari na duba yuwuwar haramta Okada a Najeriya

Bayani zai fito nan gaba

Kawo yanzu Ministan cikin gidan bai iya yin bayanin su wanene ke da hannu wajen kai harin ba, da kuma jami’an gidan gyaran halin da ake zargi da sakaci.

Legit.ng Hausa ta na sa ran cewa nan gaba za a samu cikakken labarin abinda wannan rahoto ya kunsa.

'Yan bindiga sun yi ta'adi

Idan za ku tuna, a ranar Talata, 5 ga watan Yuli 2022, aka ji labari wasu mutane da ba a san su wanene ba a lokacin, suka kai hari a babban gidan mazan na Abuja.

Wani mazaunin unguwar ya fadawa manema labarai cewa sun ga wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne su na yawo a wajen wata makaranta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel