Gwamnatin Buhari na duba yuwuwar haramta Okada a Najeriya

Gwamnatin Buhari na duba yuwuwar haramta Okada a Najeriya

  • Gwamnatin tarayya a kokarinta na magance matsalolin tsaro a kasar tana duba yuwuwar hana amfani da babura a fadin kasar
  • FG na so ta datse duk wasu hanyoyi da yan bindiga da miyagu ke bi wajen samun kudaden siyan makamai ciki harda hakar ma'adinai
  • Ministan shari'a, Abubakar Malami ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai bayan taron majalisar tsaro

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Gwamnatin tarayya na duba yiwuwar haramta amfani da babura wanda aka fi sani da Okada a fadin kasar, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Atoni Janar na tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, ne ya yi tsokacin yayin da yake jawabi ga manema labaran fadar shugaban kasa bayan taron majalisar tsaro ta kasa wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a Abuja.

Kara karanta wannan

Buhari ga 'yan Najeriya: Ku zabi Tinubu don ci gaba da shan jar miyar da nake baku

Malami ya ce bincike ya nuna cewa amfani da babura wajen gudanar da ayyukan hakar ma’adinai a fadin kasar nan kuma sanya haramcin na iya katse hanyoyin samun kudaden yan ta’adda da yan bindiga.

Okada
Yanzu Yanzu: Gwamnatin Buhari na duba yuwuwar haramta Okada a Najeriya Hoto: withinnigeria.com
Asali: UGC

Ministan wanda ya kasance tare da takwarorinsa na harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola da na harkokin yan sanda, Mohammed Dingyadi, ya ce taron ya mayar da hankali ne kan dabarun da ‘yan ta’addan ke amfani da su don dakatar da ayyukansu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce akwai bukatar gwamnati ta dauki mataki saboda yan ta’addan sun yi kaura daga hanyoyin da suka saba amfani da su wajen daukar nauyin ayyukansu zuwa hakar ma’adinai da karbar fansa.

Malami ya ce yan bindiga na amfani da babura wajen zirga-zirga, yayin da hakar ma’adinai ke samar masu da kudade don siyan makamansu.

Kan ko gwamnati za ta duba illar haramta babura da ayyukan hakar ma’adinai kan talakawan Najeriya da tattalin arziki, ministan ya ce gwamnatin tarayya za ta bayar da fifiko kan ra’ayin kasa da al’umma fiye da na ra’ayin gashin kai.

Kara karanta wannan

Ido Zai Raina Fata, Mun ba Shugaban Kasa Rahoton Fasa Gidan Yarin Kuje inji Minista

Yayin da yake magana, Aregbesola ya ce an yi kokari sosai wajen tattara bayanan sirri kafin harin da aka kai kan gidan yarin Kuje amma ya yi nadamar cewa babu damar da za a yi aiki a kan shi.

Rahoton ya kuma kawo cewa ministan, wanda ya ce an mika rahoton binciken farko kan harin ga shugaban kasar, ya ba da tabbacin cewa za a bayar da cikakken rahoto a karshen binciken.

Ya kuma bayyana cewa za a hukunta wadanda suka yi watsi da hakokin da ya rataya a wuyansu.

Legit.ng ta tuntubi wasu yan acaba don jin yadda suka dauki wannan yunkuri na gwamnati.

Mallam Dantali da ke aikin tuka babur ya ce hankalinsa ya tashi da jin wannan batu domin da wannan sana’a ta acaba ne yake daukar dawainiyar gidansa.

Ya ce:

“Muna kira ga gwamnatin Buhari da ta dube mu domin da wannan sa’a ce nake daukar dawainiyar gidana. Kin ganni nan mata biyu ga yara kuma iya wannan aiki na tuka acaba da shin a dogara. Yanzu idan aka hana ni ta ina zan samu abun ciyar da kaina da iyalina.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban SSS ya caccaki Kudirin hana Hawa Babura a Najeriya

“Gwamnati ta yi mana sassauci sannan ta nemo wani hanyar da za ta kama bata-garin cikinmu. Don yanzu shi mugu koda an toshe wannan kafar ba zai rasa wani dabaran ba.”

A bangarensa kuwa wani dan acaba mai suna Mallam Abdulhameed yace tabbass ya san gyara gwamnati ke son yi amma a dunga sara ana duba bakin gatari, yana mai cewa:

“Idan fa aka hana tuka acaba lallai barnar da hakan zai yi sai ya fi gyara. Ka duba mutum nawa ne suke dogaro da wannan a matsayin sana’a, toh idan aka ce an hana su ya kenan ake so su yi? Ai an ce laifuka su kara yawa kenan domin wani kwace zai koma yi. Kawai dai a samo wasu dabarun yakar rashin tsaro amma maganar hana acaba bata ma taso ba.”

Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar tsaro a Abuja

A baya mun kawo cewa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya jagoranci taron majalisar koli ta tsaro a fadar gwamnati da ke babban birnin tarayya Abuja, ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tinubu ya magantu a kan manyan Bishop-Bishop da aka gani a wajen gabatar da Shettima

Buhari, Sallau, babban mai taimaka wa shugaban kasa ta fannin kafafen sada zumunta ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar haɗe da Hotuna a shafinsa na Tuwita.

Taron ya samu halartar Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shugaban ma'aikatan gidan gwamnati, Farfesa Ibrahim Gambari, da kuma mai ba da shawar kan harkokin tsaro na ƙasa, Babagana Monguno.

Asali: Legit.ng

Online view pixel