Allah Ya Yiwa Tsohon Ministan Najeriya, Oluwasanmi, Rasuwa

Allah Ya Yiwa Tsohon Ministan Najeriya, Oluwasanmi, Rasuwa

  • Tsohon karamin ministan wutar lantarki da karafa, Cif Oyekunle Oluwasanmi, ya kwanta dama
  • Oluwasanmi wanda ya kuma kasance tsohon Shugaban Hukumar Kwastam na Najeriya ya mutu ne a ranar Alhamis, 21 ga watan Yuli
  • Iyalan marigayin wanda ya rasu yana da shekaru 85 ne suka sanar da labarin mutuwar nasa a cikin wata sanarwa da suka fitar

Allah ya yiwa tsohon karamin ministan wutar lantarki da karafa, Cif Oyekunle Oluwasanmi, rasuwa.

Oluwasanmi wanda ya kasance tsohon shugaban hukumar kwastam na Najeriya ya rasu ne a ranar Alhamis, 21 ga watan Yuli.

Labarin mutuwar nasa na kunshe ne a cikin wata sanarwa da iyalansa suka saki a jiya Alhamis, jaridar Leadership ta rahoto.

Oyekunle Oluwasanmi
Allah Ya Yiwa Tsohon Ministan Najeriya, Oluwasanmi, Rasuwa Hoto: Leadership
Asali: UGC

Marigayin ya kuma yi aiki a matsayin shugaban hukumar kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a shekarar 1992. Ya kuma kasance mamba a kwamitin kamfanoni da dama ciki harda Kinley Securities Limited da Wise Health Services Limited.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An yi mummunan hadari, motoci 3 sun kama da wuta, mutum 30 sun kone a hanyar Zaria zuwa Kano

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A 1995, saboda kwarewarsa wajen gudanar da ayyuka, sai gwamnatin tarayya a mulkin soja ta nada shi a matsayin mamba na kwamitin samar da jihohi da karamar hukuma. Ya kasance cikin kwamitin da ya bayar da shawarar kafa jihohin Ekiti, Ebonyi, Nasarawa, Gombe, Zamfara da Bayelsa a shekarar 1996.

An nada marigayin a matsayin karamin ministan lantarki da karafa a 1997. A karkashin kulawarsa, an samu sauye-sauye da dama wadanda suka kawo ci gaba sosai a bangaren lantarkin kasar da karafa.

Jigon al’umma wanda ya cancanci a yi koyi da shi, Oluwasanmi ya kasance Shugaban Hukumar Kwastam kuma mai kula da tashoshin jiragen ruwa na Tin Can Island da tashoshin ruwa na Calabar, jaridar The Sun ta rahoto.

Yayin da yake aikin kwastam, Oluwasanmi ya samu horo daban-daban a kasashen waje kuma ya wakilci Najeriya a taron tattaunawa kan ayyukan kwastam a kasashen Finland, Austria, Belgium, Bulgaria, Peru, Kenya da Australia.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng