Manyan Labarai A Yau
An rahoto cewa al’ummar garuruwan da yan bindiga suka aikewa takarda a kwanan nan a karamar hukumar Wase ta jihar Plateau sun tattara sun fice daga muhallinsu.
Majalisar dokokin Oyo ta tsige mataimakin gwamnan jihar, Mista Rauf Olaniyan, daga kan kujerarsa a yau Litinin, 18 ga watan Yuli. Ta zarge shi da rashin da'a.
Likitoci sun tabbatar da cewa an yi wa Farfesa Yemi Osinbajo aiki lafiya kalau a kafafun da ke damunsa, nan da ‘yan kwanaki za a salami Osinbajo, ya koma ofis.
Ademola Adeleke na PDP ya samu kuri’u 403, 371 wajen lallasa babban abokin hamayyarsa Gwamna Gboyega Oyetola na jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 375,027.
Ministan harkokin cikin gida kuma tsohon gwamnan jihar Osun, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya yi martani kan kayen da jam’iyyar APC ta sha a zaben gwamnan jihar.
Mahara sun yi garkuwa da Limaman darikar Katolika guda biyu, Rev. Fr. John Mark Cheitnum da Rev. Fr. Donatus Cleopas, a karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna.
Hedkwatar tsaro ta ce manyan kwamandojin yan ta’adda shida sun mika wuya a jihar Borno yayin da dakarun soji suka kashe mayaka 42 a yankin cikin makonni biyu.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Jigawa (SEMA) ta ce mutane shida sun mutu a sakamakon guguwar iska a yankin karamar hukumar Kafinhausa da ke jihar.
Gwamnatin tarayya ta fitar da sunayen wasu daraktoci 14 dake mataki na 17 a aikin gwamnati a ranar Laraba,13 ga watan Yuli, don nada su a matsayin Akanta Janar.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari