Saboda tsaro: An dakatar da kamfanin jiragen sama na Dana Airlines har sai baba ta gani

Saboda tsaro: An dakatar da kamfanin jiragen sama na Dana Airlines har sai baba ta gani

  • Kamfanin sufurin jiragen sama na Dana Air ya daina aiki har sai baba ta gani daga tsakar daren Laraba, 20 ga watan Yuli
  • Hukumar da ke kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya (NCAA), ta janye lasisin kamfanin Dana Airlines
  • Bincike da hukumar NCAA ta gudanar kan karfin tattalin arzikin kamfanin jiragen saman ya nuna Dana bai cika ka'idar da ta ke bukata wajen gudanar da jiragen sama ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Hukumar da ke kula da shige da ficen jiragen sama ta Najeriya (NCAA) ta dakatar da lasisin kamfanin jiragen sama na Dana Airlines har sai baba ta gani.

Matakin ya kuma fara aiki ne daga tsakar daren ranar Laraba, 20 ga watan Yuli kamar yadda hukumar ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Twitter.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kungiyar CAN Ta Nesanta Kanta Da Bishop-Bishop Da Suka Hallarci Kaddamar Da Shettima

Dana Air
Saboda tsaro: An dakatar da kamfanin jiragen sama na Dana Airlines har sai baba ta gani Hoto: channelstv

Dakatarwar ta yi daidai da sashi na 35(2), 3(b) da (4) na dokar hukumar jiragen sama, 2006 da wani sashi na 1.3.3.3(a)(1) na hukumar kula da shige da ficen jiragen saman Najeriya, 2015.

Hukuncin ya kasance sakamakon binciken da hukumar ta gudanar kan karfin kudi da tattalin arzikin gudanarwar kamfanin jiragen saman, wanda sakamakon binciken ya nuna Dana Airlines ba zai iya gudanar da hakkokin da ya rataya a wuyansa ba wajen gudanar da jiragen sama.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hukumar a cikin sanarwar dauke da sa hannun shugabanta, Kyaftin Musa Nuhu, ta bukaci fasinjoji wadanda dakatarwar za ta fi shafa da su fahimci cewa an zartar da wannan hukunci ne don bayar da kariya ga lafiyarsu, domin a cewar hukumar, ya fi bayar da muhimmanci kan lafiyar jirage sama da komai.

Jirgin Dana Air ya yi saukar gaggawa a Abuja kan wata matsala

Kara karanta wannan

Kano: Dakin Ajiya Da Wasu Wurare Sun Kone Kurmus A Gobarar Da Ta Tashi a Makarantar Yaran Ma'aikatan Jami'ar BUK

A baya mun ji cewa jirgin sama na kamfanin sufurin jiragen sama Dana Air mai lambar rijista (5N DNA) ya yi wata saukar gaggawa a filin jirgin Nnamdi Azikwe biyo bayan wata matsala da ta auku a ɗaya daga cikin injinansa.

Kamfanin sufurin ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Talata, 19 ga watan Yuli, 2022 a shafinsa na dandalin sada zumunta wato Tuwita.

A sanarwan da Kamfanin ya fitar ya nuna cewa Jirgin ya yi saukar gaggawa ne da misalin ƙarfe 2:52 na rana kuma babu wanda ya samu rauni daga cikin Fasinjojin jirgin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel