Hotunan dan tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido, yayin da ya kammala karatu da digiri mafi daraja a jami'ar UK

Hotunan dan tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido, yayin da ya kammala karatu da digiri mafi daraja a jami'ar UK

  • Barewa bata gudu danta ya yi rarrafe, Mustapha Lamido Sanusi ya kammala karatunsa a jami’ar Birtaniya da digiri mafi daraja
  • Tsohon sarkin Kano Muhammad Sanusi Lamido da iyalansa sun cika da farin ciki yayin da dansu ya kammala karatunsa a bangaren tattalin arziki
  • Mai martaba sarkin Zazzau, Malam Nuhu Bamalli yana cikin tawagar da suka halarci bikin yaye dan aminin nasa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani abun farin ciki da alfahari ya samu iyalan tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, a ranar Talata, 19 ga watan Yuli.

Hakan ya kasance ne bayan daya daga cikin ‘ya’yansa maza, Mustapha Lamido Sanusi, ya kammala karatunsa tare da samun digiri mafi daraja a bangaren tattalin arziki a jami’ar Birtaniya.

Sanusi da iyalansa
Hotunan dan tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido, yayin da ya kammala karatu da digiri mafi daraja a jami'ar UK Hoto: Linda Ikeji
Asali: UGC

Tsohon basaraken tare da mata da yaransa sun yi tattaki har kasar Birtaniya domin halartan bikin yaye daliban.

Kara karanta wannan

Yadda matashi ya sace janareto da lasifikar Masallaci a Adamawa, ya sheke kudin a tabar wiwi

Daga cikin wadanda suka halarci wannan biki harda aminin tsohon sarkin kuma Mai martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmad Nuhu Bamalli.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kalli karin hotuna wanda shafin LIB ta fitar a kasa:

Sanusi Lamido
Hotunan dan tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido, yayin da ya kammala karatu da digiri mafi daraja a jami'ar UK Hoto: Linda Ikeji
Asali: UGC

Dan sanusi
Hotunan dan tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido, yayin da ya kammala karatu da digiri mafi daraja a jami'ar UK Hoto: Linda Ikeji
Asali: UGC

Tsohon Sarki Sanusi II ya tanka masu rade-radin cewa yana goyon bayan Peter Obi

A wani labari na daban, mun ji cewa tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ya ce sam bai da hannu a wani rubutu game da ‘yan takaran 2023 da mutane suke yadawa da sunansa.

Daily Trust ta ce Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya musanya wannan ne a wani jawabi da ya fitar ta hannun hadiminsa, Malam Munir Sunusi Bayero.

Munir Sunusi Bayero wanda shi ne shugaban ma’aikatan fadar Sanusi II, ya yi watsi da rubutun da ake cewa ya nuna goyon bayansa ga Peter Obi a 2023.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kutsa Gonar Tsohon Gwamna a Najeriya, Sun Sace Mai Kula Da Gonar

Asali: Legit.ng

Online view pixel