Gabatar da Shettima: Kungiyar Kiristoci ta kalubalanci Tinubu da ya bayyana sunayen fastocin da suka je taron

Gabatar da Shettima: Kungiyar Kiristoci ta kalubalanci Tinubu da ya bayyana sunayen fastocin da suka je taron

  • Ana ci gaba da samun takaddama kan manyan limaman coci da aka gani a wajen taron gabatar da Kashim Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC
  • Kungiyar Kiristoci ta CCCN ta kalubalanci Bola Tinubu da ya bayyana sunayen limaman da suka halarci taron gabatar da Shettima don tabbatar da ingancinsu
  • Kiristoci a kasar na adawa da hukuncin APC da Tinubu na yin tikitin yan takara Musulmi da Musulmi a babban zaben kasar mai zuwa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Mambobin Kungiyar Kiristoci ta CCCN sun zargi jam’iyyar All Progresssives Congress (APC) da tara gayyar malaman addini na bogi,a wajen gabatar da dan takarar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.

Kan haka, kungiyar ta CCCN ta kalubalanci jam’iyyar da ta bayyana sunayen fastocin da cocinansu, domin a tabbatar da ingancinsu ko akasin haka, New Telegraph ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tinubu ya magantu a kan manyan Bishop-Bishop da aka gani a wajen gabatar da Shettima

Jama’a sun cika da mamaki da ganin manyan Bishop-Bishop da fastoci jere a filin taron gabatar da mataimakin Shugaban kasar na APC a Abuja.

Kashim Shettima and Bola Tinubu
Gabatar da Shettima: Kungiyar Kiristoci ta kalubalanci Tinubu da ya bayyana sunayen fastocin da suka je taron Hoto: @KashimSM
Asali: Twitter

Ana ganin an yi hakan ne domin nuna wa duniya cewa wasu kiristoci na goyon bayan tikitin Musulmi da Musulmi na APC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk da haka, kungiyar ta jaddada cewa tikitin Musulmi da Musulmi bai nuna bambancin ra’ayi da rashin zaman lafiya a kasar.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugabanta na kasa, Rev Bitrus Chollom da sakatarenta na kasa, Fasto James Alkali, kungiyar kiristocin ta yi gargadin cewa hukunci mai tsanani na jiran wadanda suke kokarin muzanta addinin.

Ta kuma sha alwashin bayyanawa duniya sunayen wadanda ke da hannu a lamarin, da nufin fallasa duk abubuwan da suka faru a taron.

Kungiyar ta ce:

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kungiyar CAN Ta Nesanta Kanta Da Bishop-Bishop Da Suka Hallarci Kaddamar Da Shettima

“Muna kalubalantar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da ya bayyanawa duniya sunayen fastoci da manyan Bishop-Bishop, wadanda basu yarda da kansu ba saboda abun da ya wakana a taron.
“Ga dukkanin wadanda abun ya shafa, muna shawartanku da ku tuba, ku yi tir da abubuwan da suka kulla taron, don hakan ya zama gyara."

Tun da farko, kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta kalubalanci jam'iyyar APC mai mulki da ta bayyana sunayen malamanta da aka ce sun halarci taron kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Tinubu ya magantu a kan manyan Bishop-Bishop da aka gani a wajen gabatar da Shettima

A gefe guda, mun kawo a baya cewa Tinubu, ya mayar da martani ga masu suka, wadanda suka zargi tawagarsa da yin hayar masu yawo a titi da kuma shirya su a matsayin malaman Kirista a wajen gabatar da abokin takararsa, Sanata Kashim Shettima a Abuja.

A cikin wata sanarwa ta hannun kungiyar yakin neman zabensa, Tinubu ya ce an bude taron ne ga kowa, ciki harda malaman addini, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Ba don ra'ayin kaina na zabi Shettima ba, Tinubu ya fadi dalilin zabo mataimakinsa

Daraktan yada muradu na kungiyar ta TCO, Bayo Onanuga ya zargi yan adawa da shiga lamarin don kai hare-hare mara amfani kan APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel