Gwamnati ta hango masifar da al’umma za ta shiga saboda tsadar kayan abinci

Gwamnati ta hango masifar da al’umma za ta shiga saboda tsadar kayan abinci

  • Gwamnatin tarayya ta hararo hadarin tsadar da kayan abinci suka yi a Najeriya da kasashen Duniya
  • Ministan harkar gona, Dr. Mohammad Abubakar ya yi wannan bayani a wajen wani taro a gairn Abuja
  • Dr. Mohammad Abubakar ya ce matsalar tsadar abinci ya shafi har kasashen waje saboda sauyin yanayi

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ankarar da jama’a a game da tsadar kayan abinci da ake fama da shi a fadin Najeriya, ta ce hakan yana da matukar hadari.

Muddin ba a dauki mataki na rage tsadar kayan abinci ba, mutane za su kara shiga cikin talauci. Vanguard ta rahoto Ministan gona yana wannan bayani.

A wajen wani taro da aka shirya a Abuja domin karawa juna sani, Dr. Mohammad Abubakar, ya nuna damuwarsa a game da yadda abinci ya ke kara tsada.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kakakin Majalisar Dokokin Wata Jiha a Najeriya Ya Rasu

Kungiyar AUDA-NEPAD ta shirya wannan taro da hadin-gwiwar jami’ar FAFU ta kasar Sin, da ma’aikatar gona domin ganin an cin ma manufofin SDG.

Abdullahi Abubakar ya wakilci Minista

Ministan harkokin gona ya gabatar da jawabi, yana mai cewa tsadar kayan abinci ya shafi kusan ko ina a Duniya, an samu hakan ne saboda sauyin yanayi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce Darektan sashen harkar gona, Abdullahi Abubakar ne ya wakilci Ministan a taron.

Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Abinci ya kara tsada a dalilin sauyin yanayi da tsadar mai, sannan ana bukatar ruwa wajen noma. A halin yanzu fari da wasu dalilai sun jawo karancin ruwa.

A cewar Ministan, ana fama da karancin wurin noma a wannan zamanin, sannan munanan yanayi sun yi sanadiyyar da amfanin gona sun ragu a ko ina.

Tashin kayan abincin a kasuwa zai sa karin mutane su shiga talauci, a rasa yadda za a samu abinci. Hakan ya sa ya zama dole gwamnati da kowa a tashi tsaye.

Kara karanta wannan

Rashin Lafiya Ya Jawo Aka Gaggauta Fita da Atiku Kasar Waje - 'Dan Kwamitin Zaben APC

A cikin kokarin da ake yi, gwamnatin tarayya na neman ganin an daina dogaro da man fetur wajen samun kudin shiga, a rungumi harkar noma gadan-gadan.

Shugabar AUDA-NEPAD a Najeriya, Gloria Akobundu, ta gabatar da jawabi, ta yi bayanin yadda za a bi domin magance karancin abinci da zaman banza.

Shirin zaben 2023

A harkar siyasa, an ji labari shugaban hukumar INEC na Najeriya, Mahmood Yakubu ya dauki alkawarin cewa zaben 2023 zai fi kowane zabe da aka taba yi.

Farfesa Mahmood Yakubu ya ce kamar yadda INEC ta shirya zabuka masu kyau a Ekiti da Osun bayan kawo sabuwar dokar zabe, za a ga gyara a badi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel