Manyan Labarai A Yau
Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da sakin tsohon sakataren Hukumar Kwallon Kafa Ta Najeriya (NFF), Sani Toro, da wasu biyu da yan bindiga suka sace.
Matashiyar budurwa, Ameerah Sufyan wacce ta yi zargin cewa an yi garkuwa da ita a shafin Twitter ta fito ta bayar da hakuri a kan kitsa labarin saceta da ta yi.
Jama'ar Najeriya na kokawa yayin da farashin gas ke kara hawa. Hukumar kididdiga ta kasa ta ce matsakaicin farashin da ake cika tukunyar gas 5kg ya kai N3,921.
Watanni biyu bayan rasuwar mai martaba Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi III, matansa Gimbiya Opeyemi Omobola da Moji sun nuna sabbin katafaren gidajensu.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnati na shirin hana amfani da kananzir a Najeriya daga shekara ta 2030 a kokarinta na hana gurbataccen iska.
Allah ya yiwa tsohon gwamnan jihohin Ribas da Filato na mulkin sojoji, Kanal Musa Sheikh Shehu mai ritaya, rasuwa a safiyar ranar Lahadi, 19 ga watan Yuni.
Musa Lurwanu Maje shi ne wanda ya labe da sunan Zahra Mansur, yana tsula tsiya a Facebook. Maje ya rika karbar kudi daga hannun jama’a ba tare da an ankara ba.
Fasinjoji goma sha takwas a wata motar bus sun kone kurmus a wani hatsarin sassafe da ya wakana a Gidan Kwano hanyar Minna-Bida a karamar hukumar Bosso, Neja.
Jam’iyyar New Nigerians Peoples Party (NNPP) ta ce daga Rabiu Kwankwaso har Peter Obi na Labour Party suna iya amincewa da zama mataimakin shugaban kasa a 2023.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari