Tsadar rayuwa: Jihohin da suka fi ko'ina tsadar gas din girki a Najeriya

Tsadar rayuwa: Jihohin da suka fi ko'ina tsadar gas din girki a Najeriya

  • Farashin gas din girki a kasuwannin cikin gida na ci gaba da tashi a fadin Najeriya kuma bai da niyan sauka
  • Wannan al’amari ya jefa yan Najeriya cikin mawuyacin hali, inda a yanzu suke neman wasu hanyoyi na daban don girka abincinsu
  • A wani rahoton baya-bayan da hukumar kididdiga ta kasa ta saki, an bayyana farashin gas inda ake cika tukunyar 5kg kan akalla N3,921.35

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Hukumar kididdiga ta kasa ta ce matsakaicin farashin da ake cika tukunyar gas din girki na 5kg ya karu zuwa 3,921.35 a watan Mayun 2022.

Hakan na kunshe ne a cikin rahoton farashin gas na watan Mayun 2022 da hukumar NBS ta saki a shafinta na Twitter.

Hukumar NBS ta ce a kan cika tukunyar ne kan naira 3,800 a watan Afrilun 2022, tana mai cewa karin ya nuna yana tashi da kaso 3.18 cikin dari a wata-wata, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

An damke mai hadawa yan Boko Haram Bam a Taraba, an gano bama-bamai 27

Bayanan hukumar kididdiga
Tsadar rayuwa: Jihohin da suka fi ko'ina tsadar gas din girki a Najeriya Hoto: NBS
Asali: Twitter

Rabe-raben yadda farashin yake a jihohi da yankunan kasar

5kg

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

  1. Farashin gas din ya fi hawa a jihar Gombe inda yake kan N4,366.67
  2. Bayalsa ta biyo baya da N4,325
  3. Adamawa da N4,250

A bangaren sauki

  1. Farashin ya fi sauki a Yobe inda yake kan N3,450
  2. Ogun - N3,450
  3. Ondo - N3,480

Yadda farashin yake a shiyoyin kasar

Mafi tsada

  1. Cika tukunyar gas na 5kg ya fi tsada a kudu maso gabas inda yake kan N4,094.39
  2. Arewa ta tsakiya N3,989.98
  3. Kudu maso kudu N3,977.72

Lamarin ya fi sauki a kudu maso yamma inda farashin yake kan N3,719.53.

Farashin gas na tukunyar 12.5kg

Wani rahoto ya ce matsakaicin farashin cika tukunyar 12.5kg na gas din girki a watan Mayun 2022 ya karu zuwa N8,726.30 a watan Mayun 2022 daga N8,164.37 a watan Afrilun 2022, wanda hakan ke wakiltan karin kaso 6.88 cikin dari na wata-wata.

Kara karanta wannan

EFCC: Yan Najeriya Sun Dena Kazar-kazar Wurin Tona Asirin Masu 'Sata' Duk La'ada Mai Tsoka Da Muke Basu

NBS ta kara da cewa:

“Hakazalika, a shekara-shekara, matsakaicin farashin cika tukunyar 12.5kg na gas ya karu da kaso 103.46 a watan Mayun 2021.”

Mafi tsada

  1. Ya fi tsada a Abuja kan N9,308.00
  2. Ekiti- N9,209.09
  3. Oyo- N9,184.06

Mafi karanci

  1. Yobe kan N7,500
  2. Kano kan N8,175.00
  3. Kogi kan N8,200

Yadda farashin yake a shiyoyin kasar

  1. Kudu maso yamma shine mafi tsada da N8,916.10
  2. Kudu maso gabas ya biyo baya N8,885.7
  3. Kudu maso kudu N8,857.09
  4. Arewa maso yamma N8,856.07
  5. Arewa ta tsakiya N8,737.57
  6. Arewa maso gabas N8,423.44

Legit Hausa ta tuntubi wasu magidanta da suka dogara da iskar gas don girki a gidajensu inda da dama suka koka kan halin da ake ciki a yanzu.

Wani magidanci mai suna Mallam Ibrahim y ace babu abin da zai ce domin a yanzu haka lamarin ya kusa zarce iyawarsa.

Ya ce:

"Abinda zan iya cewa game da tsadar gas ba abu ne mai dadi ba, domin ni gaskiya yanzu ya ma kusan fin karfi na. Watan da ya wuce gagara saye nayi, na koma amfani da gawayi amma duk da haka ban tsira ba, duk dai tsadar ce ga kuma dawainiya.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Kotu ta ci tarar wani matashi ta ɗaure shi a gidan Yari saboda rubutu kan korona a Facebook

"Abin dai sai addu'a, amma duk mai cefane kuma lebura ko mai daukar albashi, gaskiya muna shan wahala, fatanmu dai Allah ya kawo mana dauki, ya sa abubuwa su koma yadda suke ko da a da ne."

A nasa bangaren, wani mai suna mallam Muhammad ya ce shi tuni ya yanke shawarar komawa ga gawayi domin farashin gas 12kg a makon nan ya kai N11,000.

“Batun hauhawar farashin gas ba a cewa komai sai Du'a'i domin a yanzu farashin 12.5kg ya kai 11,000 a wasu yankuna.Gaskiya ko ni a yanzu na yanke shawarar komawa gawayi, toh amma nan ma sammakal! Domin kuwa gawayin ma sai ka tarfa mai kalanzir.Sai dai tashin farashin gas baya rasa nasaba da tsadar man dizil da manyan motocin dako ke amfani da shi, a yanzu litan dizil N820 yake.Rana zafi, inuwa kuna!
“Allah Ya kyauta! Allah Ya kawo mana sauki, Amin.”

Wata uwargida da ta nemi a boye sunanta ma ta koka kan wannan al'amari harma ta ce bata kaunar daura girki har sai ta ga wutan Nepa.

Kara karanta wannan

Okowa: Muhimman abubuwa 12 da baku sani ba game da abokin takarar Atiku a PDP

Ta ce:

"Aiko ana tsada fa. A ranar 8 ga watan Yuni muka cika tukunyar 12.5kg a N10,000.
"Yanzu bansan girki sai naga wutan nepa, in babu nake kunna gas."

Wata sabuwa: Gwamnatin Najeriya ta kuduri kawar da amfani da kananzir nan da 2030

A wani labarin mun ji cewa, a ranar Juma'ar da ta gabata ne shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, za a yi mai yiwuwa domin ganin 'yan Najeriya sun daina amfani da makamashin kananzir da itacen girki daga 2030.

A cewar Buhari, wannan wani bangare ne na tsare-tsaren gwamnatinsa na rage azababben hayaki mai gurbata muhalli, inji Punch.

Ya kara da cewa an mika hukumar NDC mai alhakin kula da aikin ne domin maye gurbin gudunmawar wucin gadi na ranar 27 ga Mayun bara; 2021 tsakanin Najeriya da majalisar dinkin Duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel