Majalisar dokokin jihar Kano ta zabi sabon mataimakin kakakin majalisa

Majalisar dokokin jihar Kano ta zabi sabon mataimakin kakakin majalisa

  • An zabi mamba mai wakiltan mazabar Kiru, Kabiru Hassan Dashi, a matsayin sabon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kano
  • Hakan ya biyo bayan murabus da tsohon mataimakin kakakin majalisar, Zubairu Hamza Massu, ya yi daga kujerarsa
  • Massu dai ya sauka daga kujerar ne bayan sauya sheka zuwa jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP)

Kano - Majalisar dokokin jihar Kano a ranar Litinin, 20 ga watan Yuni, ta zabi mamba mai wakiltan mazabar Kiru, Kabiru Hassan Dashi, a matsayin sabon mataimakin kakakin majalisar.

Zaben ya biyo bayan murabus da mataimakin kakakin majalisar, Zubairu Hamza Massu, dan majalisa mai wakiltan mazabar Sumaila ya yi daga matsayin.

A kwanan nan ne Massu ya sauya sheka zuwa jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP), jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Majalisar dattawa ta nada sabon shugaban marasa rinjaye

Majalisar dokokin jihar Kano
Majalisar dokokin jihar Kano ta zabi sabon mataimakin kakakin majalisa Hoto: Punch
Asali: UGC

Kakakin majalisar, Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, bayan ya karanto wasikar a yayin zaman majalisar na ranar Litinin, ya kuma ayyana kujerar mataimakin kakakin majalisar a matsayin babu kowa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan ya karanto wasikar, wani dan majalisa mai wakiltan Dawakin Tofa, Hon. Sale Marke, ya zabi Dashi sannan ya samu goyon bayan dan majalisa mai wakiltan Wudil, Hon. Nuhu Abdullahi Achika.

Dashi, wanda ya kasance tsohon mataimakin bulaliyar majalisar, mataimakin shugaban masu rijaye, kuma shugaban masu rinjaye a majalisar, ya amince da zama mataimakin kakakin majalisar, jim kadan bayan mambobin majalisar 28 sun zabe shi.

Daga nan sai ya dauki rantsuwar ofishin mataimakin kakakin majalisar, wanda daraktan shari’a na majalisar, Barista Nasidi Aliyu ya jagoranta, Daily Trust ta rahoto.

Majalisar dattawa ta nada sabon shugaban marasa rinjaye

A wani labarin, a ranar Talata ne majalisar dattawa ta nada Sanata Philip Tenimu Aduda (FCT) a matsayin sabon shugaban marasa rinjaye na majalisar, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Majisar dokokin jihar Arewa ta tsige kakakinta, da wasu 3 saboda dalilai

Haka kuma an nada Sanata Chukwuka Utazi a matsayin bulaliyar marasa rinjaye a majalisar dattawa.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ne ya sanar da nadin yayin da yake karanta wasiku daban-daban guda biyu dauke da sa hannun sakataren jam’iyyar PDP na kasa Samuel Anyanwu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng