Nadin sabbin ministoci: Na so Buhari ya dawo da Amaechi bisa dililai, Shehu Sani

Nadin sabbin ministoci: Na so Buhari ya dawo da Amaechi bisa dililai, Shehu Sani

  • Sanata Shehu Sani ya yaba da matakin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka na tura sunayen sabbin ministoci majalisa don a maye gurbinsu da wadanda suka yi murabus
  • Sai dai, tsohon sanatan mai wakiltan Kaduna ta tsakiya ya ce ya so Buhari ya dawo da ministan sufiri, Rotimi Amaechi don ya kammala ayyukan da ya fara
  • Ya kuma ce shugaban kasar bai bata lokaci ba wajen mika sunaye a wannan karon kamar yadda yake a al'adarsa na yawan jinkiri saboda ya gane cewa lokaci na shirin kure masa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Tsohon sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya ce ya so ace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake zabar Rotimi Amaechi a matsayin ministan sufuri.

Daily Trust ta rahoto cewa Sani ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 21 ga watan Yuni, a yayin hira da gidan talbijin na Channels.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Zanga-zanga ta barke a sakateriyar APC saboda adawa da zabin Tinubu

Buhari dai ya aika da sunayen mutane bakwai zuwa majalisar dattawa domin a maye gurbinsu da ministocin da suka yi murabus don neman mukaman siyasa.

Sanata Shehu Sani
Nadin sabbin ministoci: Na so Buhari ya dawo da Amaechi bisa dililai, Shehu Sani Hoto: Senator Shehu Sani
Asali: Facebook

Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufuri; Ogbonnaya Onu, tsohon ministan kimiyya da fasaha; Godswill Akpabio, tsohon ministan harkokin Neja Delta; da Emeka Nwajiuba, tsohon karamin ministan ilimi, sun ajiye aiki don neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Uche Ogah, tsohon ministan ma’adinai da karafa, ya yi murabus don neman takarar gwamnan jihar Abia, yayin da Tayo Alasoadura, tsohon karamin ministan harkokin Neja Delta, ya ajiye mukaminsa don tsayawa takarar tikitin Sanata na APC a Ondo.

Da yake martani ga zabin sabbin ministocin, tsohon satanan Kadunan ya ce shawarar da Buhari ya dauka ita ce daidai, yana mai cewa dole a ci gaba da harkokin gwamnati, jaridar The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bayan jinya a Landan, an sallami tsohon shugaban Najeriya a asibiti

Sai dai kuma ya bayyana cewa da an sake zabar Amaechi don ya kammala wasu ayyukan layin dogon da ya fara.

Ya ce:

“A ka’ida, idan aka samu gibi da murabus din ministocin da kuma shigarsu harkar siyasa, ya zama wajibi shugaban kasa ya nada sabbin ministocin da za su ci gaba da tafiyar da harkokin gwamnati da gudanar da mulki yadda ya kamata.
“Ya kasance dabi’ar shugaban kasa daukar lokaci mai tsawo kafin ya maye gurbin minista. Kamar yadda kuke gani, da yawa daga cikin wadannan ministocin sun shafe shekaru 8 suna wurin.
“Amma a wannan karon, ina jin yana sane da cewa lokaci na kure masa kuma akwai ayyukan da ba a kammala ba.
“Misali, layin doguwa karkashin Rotimi Amaechi, akwai bukatar ta samu shugaba, wanda zai ci gaba da kula da wadannan kwangiloli da yarjejeniya don a cimma abun da aka sa a gaba.
“Don haka abun da aka yi da sunayen da aka gabatarwa majalisar dattawa, ina ganin shine daidai kuma ya rage ga majalisa ta sanya rana sannan ta tantance su don su ci gaba da abun da ya kamata su yi.

Kara karanta wannan

Na lura ana neman yi mani taron dangi ne, Bola Tinubu ya fadi dalilin yi wa Buhari gori

“Na yi tunanin yadda ma’aikatar sufuri ke da muhimmanci, tsohon ministan ya yi alkawarin kammala wadannan layin dogo-wasu ayyuka a cikin shekarar nan da wasu a shekara mai zuwa.
“Da kamata yayi a dawo da shi don tabbatar da cewa wadannan kwangilolin da aka kulla da China, Portugal da sauran masu daukar nauyin ayyukan layin dogo, akalla ya ga sun kai karshe.
"Saboda al'ada ce a kasar nan, duk lokacin da aka samu sabon minista, ayyuka yawanci suna tsayawa ne lokacin da ya kamata a ci gaba da gudanar da harkoki da ayyukan gwamnati."

Yanzu-Yanzu: Buhari ya kai sunayen mutum 7 majalisa don su maye gurbin wasu ministocinsa

A gefe guda, mun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rubutawa majalisar dattawa wasika yana neman a tantance sunayen ministoci bakwai, Channels Tv ta ruwaito.

Wannan na zuwa ne tun bayan da wasu daga cikin ministocin nasa suka yi murabus tare da tsayawa takarar kujerun takara a kasar nan.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnatin Najeriya ta kuduri kawar da amfani da kananzir nan da 2030

Asali: Legit.ng

Online view pixel