Manyan Labarai A Yau
Majalisar dokokin jihar Oyo ta fara yunkurin tsige mataimakin gwamnan jihar, Rauf Olaniyan. A kwanan ne mataimakin gwamnan ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Kungiyar APC ta nemi dan takararta na shugaban kasa, Bola Tinubu, da ya duba sannan ya zabi gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello a matsayin mataimakinsa.
Daga karshe dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Bola Ahmed Tinubu ya magantu kan tikitin musulmi da musulmi da ake ta yayatawa.
Kakakin kungiyar dattawan arewa, Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa a yanzu kan talakawan Najeriya ya waye saboda haka ba sa damuwa da addinin yan takararsu.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce wasu ma’aikata a wata gona a yankin Kuje da ke Abuja sun kashe ubangidansu tare da jefar da jefar da gawarsa a cikin rijiya.
Tsohon gwamnan jihar Kebbi, Adamu Aliero ya zama dan takarar kujerar Sanata mai wakiltan Kebbi ta tsakiya karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party.
Duba ga sanarwar da INEC ta fitar, jam’iyyun siyasa 16 tare da ‘yan takararsu ne za su fafata a zaben gwamnan jihar Ekiti da za a yi a ranar 18 ga watan Yuni.
Wata matashiya yar Najeriya ta haddasa cecekuce a soshiyal midiya bayan ta wallafa cewa ta samu karin matsayi inda ta tashi daga mai aikin gida zuwa matar gida.
Bayan saukar damuna, yan gudun hijira musamman manoma daga kananan hukumomin Munya da Shiroro a jihar Neja sun fara komawa gidajensu domin komawa ga gonakinsu.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari