Yadda fasinjoji 18 suka kone kurmus a wani hatsari da afku a jihar Neja

Yadda fasinjoji 18 suka kone kurmus a wani hatsari da afku a jihar Neja

  • Hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar fasinjoji a cikin wata motar bas mai daukar mutane 18 a safiyar Lahadi, 19 ga watan Yuni
  • Lamarin ya afku ne a hanyar Minna-Bida kusa da Gidan Kwano a karamar hukumar Bosso ta jihar Neja
  • An tattaro cewa fasinjojin da ke cikin motar sun kone kurmus ta yadda ba za a iya gane su ba

Niger - Fasinjoji goma sha takwas a wata motar bus mai daukar mutane 18 sun kone kurmus a wani hatsarin sassafe da ya wakana a Gidan Kwano hanyar Minna-Bida a karamar hukumar Bosso da ke jihar Neja.

An tattaro cewa motar ta fito ne daga jihar Lagas zuwa wani wuri da ba a sani ba amma dai hukumomi sun ce ta yiwu tana a hanyarta ta zuwa Kano ko jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari Kaduna, sun sace mutane 36

Jaridar The Nation ta rahoto cewa hatsarin wanda ya afku da misalin karfe 3:00 na tsakar daren Lahadi, ya wakana ne bayan motar ta yi karo da wata babbar motar daukar kaya da aka faka a hanyar kafin ta kama da wuta.

Taswirar jihar Neja
Yadda fasinjoji 18 suka kone kurmus a wani hatsari da afku a jihar Neja Hoto: Punch
Asali: UGC

Kasancewar abun ya faru a lokacin da mutane ke bacci, an tattaro cewa ba a samu kai agaji ba har sai zuwa 5:00am lokacin da mutane suka fara taruwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Zuwa lokacin, fasinjojin sun babbake kurmus har ba a iya gane su.

The Nation ta kuma tattaro cewa an ceto biyu daga cikin mutanen sannan aka kwashe su zuwa asibtin IBB inda daya daga cikinsu ya rasu yayin da dayan ke cikin mummunan yanayi.

Jaridar Punch ta rahoto cewa kakakin yan sandan jihar Neja, DSP Abiodun Wasiu, ya tabbatar da lamarin cewa an binne mutanen a kusa da inda hatsarin ya afku.

Kara karanta wannan

Harin Kwantar Bauna: Yan Ta'adda Sun Kashe Manjo Na Soja, Sun Kona Motar Sojoji Sun Sace Makamai a Niger

Ya kuma ce lambar motar ma ta kone fiye da tunani.

Legit.ng Hausa ta tuntubi Mallam Anas Abubakar, wani mazaunin unguwar gidan magwaro inda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce abun dai sai wanda ya gani.

Ya ce:

“Gaskiya na dade ban ji tashin hankali irin wannan ba, kuma na kara tabbatarwa dan adam ba a bakin komai yake ba. An ce abun dai sai wanda ya gani domin da na dawo daga tafiya makwabcina wanda ya ga mutanen da idonsa yake sanar da ni abun da ya faru.
“Gidanmu bai da nisa da wajen hatsarin. Allah ya iya mana ya kuma ci gaba da kare mu.”

An ceto matar jigon APC da aka yi garkuwa da ita a Minna a tashar motar Kano da ke Maiduguri

A wani labari na daban, mun ji cewa an cewa an ceto matar Usman Baffa, shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), na karamar hukumar Magama da ke jihar Neja, Habiba Baffa, wacce aka yi garkuwa da ita.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Sai mun rukurkusa duk masu cin gajiyar rashin tsaron kasar nan

An dai yi garkuwa da Habiba ne a ranar Lahadi, a garin Minna, babbar birnin jihar Neja amma kuma an gano ta ne a shahararriyar tashar motar nan ta Kano da ke jihar Borno.

Kwamishinan yan sandan jihar Borno, Mista Abdu Umar, ne ya mika Misis Baffa ga iyalanta a Maiduguri a ranar Alhamis, 16 ga watan Yuni, PM News ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel