Kawancen NNPP-LP: Kwankwaso zai iya komawa mataimakin Peter Obi a zaben 2023

Kawancen NNPP-LP: Kwankwaso zai iya komawa mataimakin Peter Obi a zaben 2023

  • Jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) ta tabbatar da yiwuwar Rabiu Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano ya zama abokin takarar Peter Obi na jihar Labour Party
  • NNPP ta ce babu laifi don Kwankwaso ko Obi sun zama abokin takarar junansu gabannin zaben shugaban kasa na 2023
  • A cewar jam’iyyar, idan lokaci ya yi za a sanar da jama’a yadda tattaunawa tsakanin jam’iyyun siyasan biyu ta kaya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jam’iyyar New Nigerians Peoples Party (NNPP) ta yi martani kan wanda zai zama mataimaki a tsakanin Rabiu Kwankwaso da Peter Obi, idan aka yi maja a tsakaninsu da Labour Party.

Sakataren labaran jam’iyyar NNPP, Agbo Major, ya bayyana cewa tattaunawar hadin gwiwa tsakanin jam’iyyun biyu na gudana a yanzu haka cike da nasara.

Peter Obi and Kwankwaso
Kawancen NNPP-LP: Kwankwaso zai iya komawa mataimakin Peter Obi a zaɓen 2023 Hoto: Change Nigeria
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa Major ya tabbatar da cewar Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano na iya yarda ya zama abokin takarar Obi wanda ya kasance dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kwankwaso ya tabbatar da cewar suna kan tattaunawa da Peter Obi don hada gwiwar NNPP da LP

Major ya kara da cewa mutane da dama sun bayyana tattaunawa tsakanin shugabannin biyu a matsayin wacce za ta iya fitar da Najeriya daga halin da take ciki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Koda dai ya bayyana cewa shi ba zai so yin hasashe kan sakamakon tattaunawar ba, Major ya kara da cewar imma Kwankwaso ko Obi kowannensu na iya yarda ya zama mataimakin dayansu.

Ya ce:

“Da zaran mun gama da tattaunawar, yan Najeriya za su ji dadi, duk yadda abun ya kasance.”

Kwankwaso ya tabbatar da cewar suna kan tattaunawa da Peter Obi don hada gwiwar NNPP da LP

A baya mun kawo cewa tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Sanata Rabiu Kwankwaso, a ranar Asabar, ya tabbatar da cewar jam’iyyarsa na kan tattaunawa da jam’iyyar Labour Party da dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi.

Kara karanta wannan

Mu na tattaunawa da su Peter Obi - Kwankwaso ya tabbatar da shirin taron dangi a 2023

Ya ce suna tattaunawa ne kan yiwuwar yin maja a babban zaben shugaban kasa ta 2023 mai zuwa.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata hira da sashin Hausa na BBC a ranar Asabar, 18 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel