Sojan gona: An gurfanar da Gbajabiamila a gaban kotu kan zambar miliyoyin nairori
- An gurfanar da wani mutum da ake zargi da yiwa kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila sojan gona a gaban kotu
- An zargi mutumin wanda ainahin sunansa Suleiman Gbajabiamila da damfarar wani dan Najeriya mazaunin Turai kudi har naira miliyan 30
- Sai dai kuma bai amsa tuhumar da ake mas aba wanda ke da alaka da sata da kuma gabatar da karairayi
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Lagas - Yan sanda a ranar Litinin, 20 ga watan Yuni, sun gurfanar da Suleiman Gbajabiamila mai shekaru 62 a gaban babbar kotun majistare ta 1, Yaba Lagas.
An gurfanar Gbajabiamila ne kan zargin damfarar wani dan Najeriya mazaunin Turai, , Lateef Adeyemo, kudi har naira miliyan 30.
Jaridar The Guardian ta rahoto cewa Gbajabiamila ya shafe tsawon watanni yana wasan yar buya kafin aka kama shi sannan aka gurfanar da shi a gaban alkalin kotun majistare, Adeola Olatunbosun.
Ana dai tuhumar sa ne kan abubuwa biyu da suka hada da sata da karya wajen gabatar da kansa, laifin da hukuncinsa ke karkashin sashi na 287 na dokar laifi na jihar Lagas 2015.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Dan sanda mai kara, ASO Folorunso ne ya gabatar da mai laifin a gaban kotu. A bisa ga tuhumar, Gbajabiamila ya gabatar da kansa a matsayin dillalin gidaje a shekarar da ta gabata, inda ya karba naira miliyan 30 da aka ware domin siyawa Adeyemo wani gida mai daki biyu tsakanin Satumba da Oktoban 2021.
Sai dai wanda ake zargin bai amsa tuhumar da ake masa ba sannan an tsare shi a hannun yan sanda.
Alkali Olatunbosun ya dage sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Yulin 2022.
Da yake zantawa da The Guardian bayan zaman, Adeyemo ya ce Gbajabiamila ya dade yana amfani da sunan kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila wajen damfarar mutane da dama kuma ya shafe tsawon watanni yana wasar yar buya kafin aka kama shi.
Ya ce:
“Na san shi ne ta hannun wasu mutane biyu sannan na fara tura masa kudi. Harma ya nuna mana makullin gidan da hotuna kuma ban taba zarginsa ba da farko.
“Na gane cewa ya damfare ni ne lokacin da ya daina daukar wayanmu a January 2022. Daga baya sai mutumin da ya hada ni da shi yace kada na damu saboda dan uwan kakakin majalisar wakilai ne.
“Ban taba sanin cewa barawo bane. Ya shirya mun takardar kudi na bogi lokacin da na nemi ya dawo mani da kudina sannan ya ce ya biya kudin.
“Gaba daya kudin naira miliyan 31 ne saboda sun karbi naira miliyan 1 a matsayin tukwici, amma ba a saka shi ciki ba.”
Da gangan na fita daga gidanmu: Ameerah Sufyan ta nemi afuwar jama’a kan kitsa garkuwa da kanta da ta yi
A wani labari na daban, matashiyar budurwa, Ameerah Sufyan wacce ta yi zargin cewa an yi garkuwa da ita a shafin Twitter a makon da ya gabata ta fito ta bayar da hakuri a kan kitsa lamarin da ta yi da kanta.
Da farko mun ji cewa Ameerah ta je shafin Twitter inda ta yi zargin cewa yan bindiga sun yi garkuwa da ita da wasu mutane 16 a yankuna daban-daban na Abuja.
Sai dai kuma, rundunar yan sandan birnin tarayya wacce ta gano matashiyar kwanaki uku bayan ta yi kokawar ta karyata ikirarin cewa an sace ta ne.
Asali: Legit.ng