Da dumi-dumi: Yan bindiga sun sako tsohon Sakataren Hukumar NFF, Sani Toro da wasu 2

Da dumi-dumi: Yan bindiga sun sako tsohon Sakataren Hukumar NFF, Sani Toro da wasu 2

  • Rundunar yan sanda a jihar Bauchi ta tabbatar da kubutar tsohon sakataren Hukumar Kwallon Kafa Ta Najeriya (NFF), Sani Toro daga hannun yan bindiga
  • Hakazalika maharan sun sako tsohon mataimakin kocin Super Eagles, Garba Yila da Alhaji Isa Jah wadanda aka sace tare da shi
  • Sai dai kuma, kakakin yan sandan, Sp Ahmed Wakil, ya ce zuwa yanzu babu wani cikakken bayani kan yadda aka sake su

Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da sakin tsohon sakataren Hukumar Kwallon Kafa Ta Najeriya (NFF), Sani Toro, tsohon mataimakin kocin Super Eagles, Garba Yila da Alhaji Isa Jah.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta rahoto cewa rundunar yan sandan ta ce yan bindiga da suka yi garkuwa da su ne suka sako su.

Sani Toro
Da dumi-dumi: Yan bindiga sun sako tsohon Sakataren Hukumar NFF, Sani Toro da wasu 2 Hoto: @PremiumTimesNg
Asali: Twitter

Kakakin yan sandan, Sp Ahmed Wakil, wanda ya tabbatar da sakin nasu ga manema labarai a jihar Bauchi a ranar Talata, 21 ga watan Yuni, ya ce babu cikakken bayani kan yadda aka sake su a yanzu haka, jaridar The Sun ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar NNPP da Kwankwaso sun gamu da cikas a hanya daga bangaren Shekarau

Wani makusancin Toro, Mista Aliyu Guman ma ya fadama NAN cewa an saki dukkaninsu a safiyar yau Talata da misalin karfe 5:00 na asubahi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:
“An mayar da su Abuja don su hita sannan a duba lafiyarsu amma suna cikin koshin lafiya, mun gode ma Allah kan haka.
“Tuni aka sada su da yan uwansu a Bauchi.”

Masu Garkuwa Sun Sace Tsohon Sakataren Hukumar NFF, Sani Toro

A baya mun ji cewa yan bindiga sun sace tsohon sakataren Hukumar Ƙwallon Kafa Ta Najeriya, NFF, Sani Toro, Premium Times ta rahoto.

An sace tsohon sakataren na NFF ne a hanyarsa ta komawa Bauchi daga Abuja inda ya hallarci daurin auren dan tsohon shugaban NFF Aminu Maigari.

Kakakin yan sandan Jihar Bauchi, Ahmed Wakil, ya tabbatar wa Premium Times sace shin, amma ya ce ba shi da cikakken bayanin tunda abin ba a Bauchi ya faru ba.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindiga sun sako shugaban kauye don ya tara N100m ya karbi mutanensa 30

Asali: Legit.ng

Online view pixel