Likafa ta ci gaba: Matan marigayi Alaafin na Oyo sun baje kolin sabbin gidajen da suka mallaka

Likafa ta ci gaba: Matan marigayi Alaafin na Oyo sun baje kolin sabbin gidajen da suka mallaka

  • Watanni biyu bayan rasuwar Alaafin na Oyo, abun farin ciki ya samu wasu daga cikin matan marigayi sarkin daular Yarbawan
  • Biyu daga cikin matan marigayi sarkin sun je shafin soshiyal midiya domin jinjina masa tare da godiya gare shi kan yadda yake kula da su har bayan ransa
  • Sun kuma wallafa hotunan gidajen da marigayin ya yi masu tanadinsu kuma aka mallaka masu shi a lokacin da suke tsananin bukata

Ibadan - Kimannin watanni biyu bayan rasuwar Alaafin na Oyo, Lamidi Adeyemi III, matansa Gimbiya Opeyemi Omobola da Moji sun nuna sabbin katafaren gidajensu.

Matan marigayi sarkin wadanda suka cika da godiya sun jinjina masa tare da addu’an Allah ya ji kansa.

Marigayi Alaafi na Oyo matansa da sabbin gidajensu
Likafa ta ci gaba: Matan marigayi Alaafin na Oyo sun baje kolin sabbin gidajen da suka mallaka Hoto: @queenmoji_gloo/@queenomobolanle
Asali: Instagram

Moji ta gode ma marigayi Alaafin sannan ta tabbatar da cewar mutuwarsa ta zo kwatsam amma tarihin da ya kafa zai ci gaba da wanzuwa.

Kara karanta wannan

Mutanen gari sun yi farin ciki, an tsinci gawawwakin ‘yan ta’adda jibge a cikin rafi

Ta rubuta a shafinta:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ina son amfani da wannan damar don godema mijina sarkina kuma ubana kan wannan katafaren kyauta nagida. Ya zo mana a kwatsam amma Allah ya san abun da ya fi dacewa mun yi kewarka, muna kaunarka, amma Allah ya fi mu son ka. Allah ya sa tarihin da ka kafa ya ci gaba da wanzuwa ya sarkina. Allah ya ji kanka kabiesi @alaafin_oyo Omo ibironke."

Da take wallafa hotunan katafaren gidan nata da kuma hotunanta tare da marigayin mijinta a nata bangaren, Gimbiya Opeyemi ta ce soyayyarta gare shi bai da iyaka.

Ta yi masa godiya a kan tarin kyaututtukan da ta more daga gare shi.

The Nation ta nakalto gimbiyar na cewa:

"Godiya: dan takaitaccen godiya ta ga Mai Martaba Sarki!!!
“Kowace rana, nakan farka da tunanin mijina da tasirinsa a gare ni kafin rasuwarsa, ina godiya ga Allah.

Kara karanta wannan

Bidiyon tsofafin jaruman kanywood a wajen shagalin sunan tsohuwar jaruma Fati Ladan

“Wannan na daya daga cikin kyaututtukan da Mai Martaba Sarki Iku Baba Yeye ya ba ni. Ban yi tsammanin kyautar gida mai kyau ba, amma mijina da ya rasu ya sa hakan ta faru.
“Har ila yau, godiyata bata da iyaka. Har abada, soyayyata gareka bata da iyaka. Allah ji kanka a duk inda kake, ya kai mijina.
“Ka ci gaba da hutawa, Adeyemi Atanda. Na gode sosai.”

Da take taya kanta murnar samun sabon gida, ta kara da cewa:

“Ina mai taya kaina murna. Sabon gida, sabon nasara, sabon tunani, Nagode mijina na kaina. Allah ya ji kanka da rahama.”

Da take wallafa nata hotunan tare da marigayi sarkin da sabon gidanta, Gimbiya Opeyemi Omobola ta tuna yadda ta isa fadar a matsayin ba kowa ba amma ta zama Gimbiya.

Ta gode ma marigayi sarkin kan sauya rayuwarta da ya yi tare da mata kyautar gida a lokacin da take tsananin bukata.

Kara karanta wannan

Mutane 5 sun mutu yayinda aka yi karo tsakanin yan IPOB da wata kungiyar hamayya a Anambra

Wani bangare na jawabin nata ya ce:

“Yana da matukar wahala bayyana yadda karamcinka ya taimake mu a lokacin da muke tsakanin bukata. Samun tuni daga mutanen da suka damu da mu cewa ba mu kadai bane a lokacin da muke juyayiba karamin abu bane.
“Wannan ya tuna mani da ranar da na shigo fadarka a matsayin ba kowa ba ba tare da sanin cewa tarin kyawawan abubuwa za su faru a lokacin da mace ta hadu da mahadin rayuwarta.
“Ka mayar da ni mutum mai daraja a lokacin da kake raye sannan harma ka yi mun tanadin kyauta mai daraja da kowani mutum mai rai ke addu’an mallaka, wanda shine gida, kuma ba wai gida kawai ba a’a dan karamin Faris ne a nahiyar Afrika.”

Bidiyon tsofafin jaruman kanywood a wajen shagalin sunan tsohuwar jaruma Fati Ladan

A gefe guda, tsohuwar jarumar masa’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Fati Ladan, ta samu karuwar diya mace a gidan aurenta.

Kara karanta wannan

Budurwa Mai Shagon Askin Da Mata Ke Wa Maza Rawa da Tausa, Tace Ba Kai Kadai Suke Askewa Ba

Tuni dai aka yi shagalin suna na gani na fada, taron da ya samu halartan manyan tsoffin jaruman masana’antar da suka yi mata kara.

A cikin wani bidiyo da shafin mufeeda_rasheed1 ta wallafa an Instagram an gano tsoffin jarumar kamar su Sadiya Gyale, Fauziyya Mai kyau, Fati KK, Wasila da sauransu suna taya mai jego rawa tare da yi mata likin kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel