Manyan Labarai A Yau
Babban faston nan na cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), Enoch Adeboye, ya ce bai taba umurtan kowa da ya siya bindiga da sunan zai kare kansa ba.
Omoyele Sowore ya fitar da wanda zai sa ya kai labari a zaben shugaban kasa. AAC ta na sa ran Haruna Magashi zai taimaka mata wajen yin galaba a kan APC da NNPP
Beatrice ta bukaci kotu da ta bari ta gurfana a gefen mijinta saboda basu ga junansu ba tun bayan zaman karshe da aka yi a makon jiya. Sai dai kotu ta hana ta.
Jam’iyyar PDP reshen jihar Borno a ranar Alhamis, 30 ga watan Yuni, ta dakatar da shugabanta, Alhaji Zannah Gadama, kan zarginsa da yiwa jam'iyyar zagon kasa.
Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ta kaddamar da kwamitin yakin neman zabenta na gwamnan jihar Osun. Sai dai kuma yawancin gwamnoninta basu hallara ba.
Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya zargi shugabannin addinai da basu san abun da ya kamata ba da haifar da rikicin addini da rashin hadin kai.
Tun 2019 Lauyoyin EFCC su ka fara binciken Bukola Saraki bisa zargin ya saci kudi daga gwamnati. Shekaru uku kenan har yau ba a yanke hukunci a shari’a ba.
Daruruwan maniyyata aikin hajji a jihar Kano na gudanar da zanga-zanga a Kano kan hana su kujerar hajji duk da cewar sun biya cikakken kudi na hajjin bana.
Sarkin Minna Alhaji Umaru Faruk Bahago, ya shiga lamarin rikici tsakanin kwamishinan yan sandan jihar Neja, Monday Bala Kuryad da kwamandan kungiyar yan banga.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari