Maniyyata aikin hajji sun gudanar da zanga-zanga a Kano kan hana su kujera

Maniyyata aikin hajji sun gudanar da zanga-zanga a Kano kan hana su kujera

  • Maniyyata aikin hajji sun gudanar da zanga-zanga a ofishin hukumar alhazai ta jihar Kano kan hana su kujera a bana
  • Fusatattun masu zanga-zangar sun bayyana cewa wasu daga cikinsu sun shiga shirin tara kudin zuwa hajjin tun a shekarar 2019
  • Sai dai kuma, babban sakataren hukumar alhazai ta Kano, Abba Dambatta, ya bayyana cewa hukumar na iya bakin kokarinta don magance matsalar

Kano - Daruruwan maniyyata aikin hajji na gudanar da zanga-zanga a garin Kano kan hana su kujerar hajji duk da cewar sun biya cikakken kudi na hajjin bana.

Masu zanga-zangar sun mamaye babban ofishin bakin zamani da suka biya kudadensu ta wani shirin tanadi, da kuma ofishin hukumar aikin hajji ta jihar Kano, Daily Trust ta rahoto.

Mutanen da abun ya shafa wanda adadinsu ya kai 284 sun bayyana cewa sun kadu bayan sun gano cewa ba a tanadar masu kujeru ba bayan biyan kudin da suka yi, suna masu cewa tun a 2019 wasun su suka shiga shirin tanadin.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An kama wanda ya harbe tsohon hadimin Jonathan, Ahmad Gulak

Maniyyata
Maniyyata aikin hajji sun gudanar da zanga-zanga a Kano kan hana su kujera Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa an kwashi rukunin farko na maniyyata daga jihar Kano zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin hajjin 2022 a ranar Litinin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daya daga cikin maniyyatan, Auwalu Jibrin ya ce:

“Mune wadanda hukumar aikin hajji ta kasa ta bukace mu da mu bude asusu tare da bankin Jaiz sannan mu ajiye kudadenmu a nan. Hukumar aikin hajji ta jiha ta karbi fasfo dinmu sannan ta tantance mu amma kuma yanzu mun ji cewa ba a bamu kujeru ba.
“A yanzu an barmu a makale ba tare da wani tabbaci ba. Bankin Jaiz ta fada mana cewa babu matsala kuma suna aiki don magance matsalar.”

Majiyoyi da ke da masaniya kan ci gaban sun bayyana cewa an tura sunayen fusatattun maniyyatan zuwa ga hukumar aikin hajji ta jiha amma ba a sanyasu a cikin aikin hajjin bana ba saboda an rage yawan kujerun da aka bayar.

Kara karanta wannan

Sokoto: 'Yan Bindiga Sun Halaka Manoma 11, Sun Kallafawa Wasu Harajin Noma

A cewar wata majiya, hukumar aikin hajji ta jihar ta takura da sama da sunaye 100 da NAHCON ta aika mata domin a basu kujeru yayin da dama da suka shafe shekaru suna tara kudi karkashin shirin basu samu wuri ba.

A bangarensa, babban sakataren hukumar alhazai ta Kano, Abba Dambatta, ya fada ma Daily Trust cewa hukumar na iya bakin kokarinta don magance matsalar, yama mai cewa babu kujera ga wadanda ke shirin tanadi a wannan shekarar, musamman ma wadanda ke karkashin bankin Jaiz.

Sai dai kuma ya ce zai je Abuja don kokarin ganin ya nemawa maniyyatan 184 kujeru.

Dhul-Hijjah: Sarkin Musulmi ya umarci a fara duban jinjirin watan babbar Sallah

A wani labarin, Sarkin Musulmai kuma shugaban majalisar Ƙoli ta shari'ar musulunci a Najeriya (NSCIA), Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya umarci ɗaukacin al'ummar Musulmi su fara duban jinjirin watan Dhul Hijjah daga ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kashe Yan Bijilante Da Mafarauta 6 Da Suka Tafi Daji Don Ceto Manoma 22 Da Aka Sace a Niger

Sultan Abubakar ya ba da umarnin ne a wata sanarwa da kwamitin duban wata ya fitar a shafinsa na Facebook ɗauke da sa hannun Farfesa Sambo Junaidu, shugaban kwamitin shawarwari kan harkokin Musulunci.

Sanarwar ta tunatar da al'umma cewa ranar Laraba, 29 ga watan Dhil-Qa'adah, 1443 wacce ta zo dai-dai da 29 ga watan Yuni, 2022, ita ce ranar farko da ya kamata a duba wata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel