Ban ce kiristoci su siya bindigogi don kare kansu ba – Babban faston Najeriya ya yi karin haske
- Babban faston cocin RCCG ya yi karin haske kan rahotannin cewa ya bukaci kiristoci da su kare kansu
- Fasto Adeboye ya bayyana cewa bai bukaci kowa ya siya bindiga ba don kiristoci ba za su so kashe kowa ba
- Sai dai kuma, malamin addinin ya ce duk wani makiyin da ya zo kusa da coci zai tarar da Allah a kofar shiga
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Babban faston cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), Enoch Adeboye, ya ce bai taba umurtan kowa da ya siya bindiga don kare kansa ba.
Da yake jawabi a taron godiya ga Allah na sabon wata a cocin a ranar Lahadi, 3 ga watan Yuli, malamin ya ce bai umarci kowa da ya yi amfani da bindiga ba, jaridar Vanguard ta rahoto.
Ya ce:
“Ban taba umurtan Kiristoci da su je su sayi bindigogi ba. Samson a cikin Littafin Injila bai yi yaki da bindigogi ba. Ya yi amfani da kashin gatari kuma ta yaya za ka yiwa yara bayanin haka? Ka nuna musu kashin gatari."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya yi karin hasken ne bayan wasu rahotannin kafofin watsa labarai cewa shi ya nemi ayi “wuta-wuta” ga duk wani hari da aka kai kan kiristoci.
“Kada ku siya bindigogi. Ba za ku so kashe kowa ba. Kawai dai ya zama dole mu tabbatar da ganin cewa bakin da bama so basu zo cocinanmu ba, don haka kada ku je ku siya bindigogi.”
Adeboye ya kuma karfafawa taron jama’ar gwiwar cewa kada su ji tsoron halartan tarukan coci saboda harin da yan ta’addan suka kai coci a Owo, jihar Ondo.
Babban Faston Najeriya Ya Bayyana Abin Da Zai Faru Da Duk Wanda Ya Yi Wa Annabi Isa Batanci
A baya mun ji cewa Fasto Adeboye, ya yi gargadin cewa duk wanda ya yi batanci ga Annabi Isa (AS) zai dandana fushin Ubangiji, rahoton The Punch.
Adeboye, wanda ya yi jawabi a taron RCCG na watan Yuli, ranar Juma'a/Asabar ya yi wannan maganan ne yayin martani kan hare-haren da ake kai wa coci-coci a sassan kasar.
Religion Nigeria ta rahoto cewa a kalla mutum 40 ne yan darikar Katolika yan bindiga suka kashe a watan Yuni a Owo, Jihar Ondo.
Asali: Legit.ng