Osinbajo ya bayyana ainahin wadanda ke haddasa rikicin addinai a Najeriya

Osinbajo ya bayyana ainahin wadanda ke haddasa rikicin addinai a Najeriya

  • Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce ana samun tashe-tashen hankula tsakanin addinai a Najeriya ne idan shugabanni basu yi abun da ya kamata ba
  • Osinbajo ya bayyana hakan ne yayin da ya gana da shugabannin addinai a fadar shugaban kasa a ranar Laraba, 29 ga watan Yuni
  • Osinbajo ya ce kasar na fuskantar matsalar hada kan yan al’ummarta mabiya addinai daban-daban da kuma kabilanci

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya zargi shugabannin addinai da basu san abun da ya kamata ba da haifar da rikicin addini da kuma rashin hadin kai a kasar nan.

Osinbajo ya bayyana hakan ne yayin da wata tawaga daga kungiyar addinai ta Kuje karkashin jagorancin Sam Ogbodo, wani babban fasto na cocin Palace Church International, suka ziyarce shi a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Abinda Muka Tattauna da Obasanjo Yayin da ya Kawo Min Ziyara, Ango Abdullahi

Yemi Osinbanjo
Osinbajo ya bayyana ainahin wadanda ke haddasa rikicin addinai a Najeriya Hoto: Professor Yemi Osinbajo
Asali: Facebook

Mataimakin shugaban kasar ya fada ma tawagar cewa daya daga cikin manyan matsalolin da ya kamata kasar nan ta fuskanta shine hadin kan mutane, hadin kan kabilu da na addinai, Channels Television ta rahoto.

A cewarsa, ta hakan ne za a samu ainahin ci gaba a bangarori daban-daban na kasar da ke bukatar ci gaba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata sanarwa daga Laolu Akande, kakakin mataimakin shugaban kasar ya nakalto ubangidan nasa na cewa:

“Daya daga cikin tangardar da muke da shi shine rabuwar kawuna ta bangaren addini da kuma tashin hankalin da hakan ke haddasawa idan shugabannin addinai suka gaza yin abun da ya kamata don hada mabiya addinai daban-daban.
“Ina matukar farin ciki da abun da kuke yi. Kungiyar addinai a Kuje ba wai kawai madubin dubawa bane ga wannan yankin, madubun dubawa ne ga kasar nan.”

Kara karanta wannan

Za mu durkusa a gaban Wike idan hakan zai sa ya ci gaba da zama a PDP, in ji Walid Jibrin

Ya jinjinawa tawagar kan sanar da gwamnati wasu muhimman batutuwa, yana mai cewa gwamnati ta jajirce don isar da ci gaba mai dorewa, rahoton The Cable.

Ya kara da cewa:

"Kuma ina zaton abin farin ciki ne ganin yadda kuka kalli hakan a matsayin abu mai muhimmanci, da kuma yadda kuke yin duk abin da za ku iya don tabbatar da ganin cewa mun mai da hankali kan abin da ke da mahimmanci ga mutane.”

Mataimakin shugaban kasar ya jadadda cewa kowa na da yancin yin addininsa, a kundin tsarin mulki, akwai yancin bauta, amma shugabanni ne dole za su isar da muhimman abubuwa, ya zama dole gwamnati ta isar da aiki kan batutuwan ci gaba.

FG: 'Yan Ta'adda ne ke Zagon-Kasa ga Wutar Lantarkin Yankin Arewa Maso Gabas

A wani labarin, gwamnatin tarayya ta ce 'yan ta'adda ne ke kawo ci baya a kokarin da ake na samar da tsayayyar wutar lantarki mai dorewa ga 'yan Najeriya, musamman yankin arewa maso gabas.

Kara karanta wannan

Mun Baka Awa 48: PDP Za Ta Yi Wa Obasanjo Fallasa Idan Bai Yi Karin Haske Kan Maganan Da Ya Yi Kan Atiku Ba

Ministan wutar lantarki, Abubakar Aliyu ya fadi hakan bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar shugaban kasa Villa da ke Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Ya bayyana yadda FEC ta amince da kwangilolin wuta da ruwa da dama wadanda suka kai kimar N23,047,974,090.

Asali: Legit.ng

Online view pixel