Manyan Labarai A Yau
Dan mai martaba tsohon sarkin Kano, Mustapha Lamido Sanusi, ya kammala karatunsainda ya samu digiri mafi daraja a bangaren tattalin arziki a jami’ar Birtaniya.
Yan sanda sun kama wani matashi, Umar Sani, sun gurfanar da shi kan zargin satar injin janareto da lasifikan wani Masallaci a Yola, babban birnin jihar Adamawa.
Gwamnatin tarayya ta hararo hadarin tsadar da kayan abinci suka yi a yau. Minista ya ce tsadar abinci zai kara jefa mutane a talauci idan ba a dauki mataki ba.
Kwanaki kungiyar Kano First Forum ta nemi a hana Gwamna Abdullahi Umar Ganduje cin bashi. A jiya Alkali ya halattawa Gwamnatin Ganduje karbo danyen bashin.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari cike da barkwanci ya zolayi shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, inda ya bukace shi da ya juyo ya kalle shi a wani taro.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) da a babbar birnin tarayya Abuja a ranar Talata, 19 ga watan Yuli.
Jami'an tsaro na Hisbah a jihar Kano sun yiwa wani matashi askin kwalkwabo sakamakon tara gashi da ya yi a kansa. Sai dai hakan bai yiwa wasu da dama dadi ba.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar , yana cikin koshin lafiya, cewar mai taimaka masa a kan harkokin yada labarai, Paul Ibe.
Rundunar yan sandan jihar Katsina tana neman shugaban yan bindiga, Ado Aleru, wanda Sarkin Yandoto ya nadawa sarautar Sarkin Fulani a ranar Asabar ruwa a jallo.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari