Rundunar yan sanda ta ayyana neman shugaban yan bindiga, Ado Aleru, ruwa a jallo

Rundunar yan sanda ta ayyana neman shugaban yan bindiga, Ado Aleru, ruwa a jallo

  • Duk wanda ya kamo ko ya bayar da bayani kan inda shugaban yan bindiga, Ado Aleru, yake zai samu kyautar naira miliyan 5
  • Rundunar yan sandan jihar Katsina ta ayyana neman Aleru ruwa a jallo kan zarginsa da kashe sama da mutum 100
  • A ranar Asabar ne dai Sarkin Yandoton Daji, Aliyu Marafa, ya nada gogarmar dan ta’addan sarautar Sarkin Fulani

Katsina - Rundunar yan sandan jihar Katsina ta ayyana neman gogarmar dan bindiga, Ado Aleru, wanda Sarkin Yandoto na Zamfara ya nadawa sarautar Sarkin Fulani a ranar Asabar ruwa a jallo.

Ana neman Aleiro ne kan zargin aikata ayyukan ta’addanci ciki harda kashe akalla mutane 100, jaridar Vanguard ta rahoto.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar da Sarkin Yandoton Daji, Aliyu Marafa, kan nadawa dan ta’addan da ake nema ruwa jallo sarauta.

Kara karanta wannan

Nada dan bindiga sarauta: Har yanzu Katsina ba ta yafe wa Ado Aliero ba - Masari

Aleru
Rundunar yan sanda ta ayyana neman shugaban yan bindiga, Ado Aleru, ruwa a jallo Hoto: Sahara Reporters
Asali: UGC

Kakakin yan sandan jihar Katsina, Gambo Isa, ya ce duk wanda ya kama ko ya bayar da bayanan da za su kai ga kama gogarmar dan bindigar, zai samu kyautar naira miliyan 5, yana mai cewa dan ta’addan ya kashe fiye da mutane 100 a jihar Katsina ciki harda mata da yara, Channels TV ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma bayyana cewa Aleiro na cikin yan bindigar da rundunar ke nema saboda ya kashe tare da sace mutane da dama.

A cewarsa:

“Muna neman Aleru ne saboda ayyukan ta’addanci da ya aikata a garin Kadiso inda ya kashe mazauna kauyen fiye da 100. Mun kasance tare da kwamishinan yan sanda, Sanusi Buba da yan jarida a Kadiso inda muka ga yadda ya kashe mutane ciki harda mata da yara, da kuma lalata kayayyakin abinci da dabbobi.

Kara karanta wannan

Karfin hali: An cafke wani dan shekara 60 da ya tsere daga gidan yarin Kuje a Kaduna

“Hakan ne ya sa rundunar ‘yan sandan Katsina ta fitar da sanarwar cewa duk wanda ya kama Aleiro ko a mace ko a raye za a ba shi naira miliyan 5. Wannan al'amari yana nan. Muna nemansa kuma duk wanda ya ganshi ya kawo mana rahoto. Muna tuhumar sa da aikata ta’addanci a Kadiso, da sauran garuruwa ma. Ya kuma yi garkuwa da mutane sannan ya karbi kudin fansa.”

Nada dan bindiga sarauta: Har yanzu Katsina ba ta yafe wa Ado Aliero ba - Masari

A baya mun ji cewa gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa har yanzu bata yafewa Ado Aleiro, dan bindigar da take nema ruwa a jallo ba.

A ranar Lahadi, 17 ga watan Yuli ne aka yiwa Aleiro wanda ya kasance rikakken dan ta'adda nadin sarautar Sarkin Fulani a masarautar 'Yandoton daji dake jihar Zamfara.

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya shaidawa sashin BBC Hausa cewa sun kadu matuka da jin labarin nadin sarautar da aka yiwa Aleiro.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya kaddamar da Mataimaki, ya ce ya dauko wanda za su gyara Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel