Manyan Labarai A Yau
Ministan harkokin cikin gida kuma tsohon gwamnan jihar Osun, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya yi martani kan kayen da jam’iyyar APC ta sha a zaben gwamnan jihar.
Mahara sun yi garkuwa da Limaman darikar Katolika guda biyu, Rev. Fr. John Mark Cheitnum da Rev. Fr. Donatus Cleopas, a karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna.
Hedkwatar tsaro ta ce manyan kwamandojin yan ta’adda shida sun mika wuya a jihar Borno yayin da dakarun soji suka kashe mayaka 42 a yankin cikin makonni biyu.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Jigawa (SEMA) ta ce mutane shida sun mutu a sakamakon guguwar iska a yankin karamar hukumar Kafinhausa da ke jihar.
Gwamnatin tarayya ta fitar da sunayen wasu daraktoci 14 dake mataki na 17 a aikin gwamnati a ranar Laraba,13 ga watan Yuli, don nada su a matsayin Akanta Janar.
Dazu Muhammadu Buhari ya yi huduba da ya ziyarci Sarkin Daura a karon karshe a matsayin Shugaban Najeriya, ya ce babban abin da ya bar wa yaran shi ne ilmi.
A cikin hoton, an gano Gwamna Bello Matawalle a tsakanin kyawawan yaransa maza inda kowannensu ke sanye da tufafi iri guda na farar shadda dinkin babban riga.
'Yan sanda a Ogun a ranar Laraba, 13 ga watan Yuli, ta bayyana cewa ta kama wani da ya tsere daga gidan yarin Kuje, Yakubu Abdulmumuni, a yankin Sango-Ota.
Allah ya yiwa dan majalisar dokokin jihar Oyo, Ademola Olusegun Popoola, rasuwa a safiyar yau Laraba, 13 ga watan Yuli, bayan ya yi fama da rashin lafiyaa.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari