Bidiyon yadda yan Hisbah suka kama wani matashi da ya tara gashi, suka yi masa askin kwalkwabo

Bidiyon yadda yan Hisbah suka kama wani matashi da ya tara gashi, suka yi masa askin kwalkwabo

  • Wani matashin saurayi ya taki rashin sa'a inda aka kwalkwale masa tulin gashin da ya tara a kansa
  • Jami'an Hisbah a jihar Kano sun cika hannu da wani saurayi da ya tara gashi inda suka yi masa askin kwalkwabo
  • Mutane da dama na ganin ba a kauyatawa saurayin ba saboda a cewarsu ko addini bata haramta tara gashi ba ga da namiji

Kano - Wani matashin saurayi ya fada komadan jami’an tsaro na Hisbah a jihar Kano sakamakon tara gashi da ya yi.

A cikin wani bidiyo da shafin beautifull_people_of_arewa ya wallafa a kafar sadarwa ta Instagram, an gano wani mai aski yana kwalwalewa matashin gashin da ya tara.

Lamarin dai ya faru ne a gefen titi kuma a bainar jama’a yayin da aka gano wasu jami’an Hisbah daga gefe suna saka ido a askin da ake yi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun sace wani babban Basarake a arewa

Yan Hisbah
Bidiyon yadda yan Hisbah suka kama wani matashi da ya tara gashi, suka yi masa askin kwalkwabo Hoto: Vanguard/Instagram/beautifull_people_of_arewa
Asali: UGC

Hakazalika, an jiyo muryar wanda ke nadar bidiyon abun da ke faruwa yana cewa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mallam Sals, Hisbah aikin Allah. Ma shaa Allah! Ma shaa Allah!! Alhamdulillahi, Mashaa Allah godiya yake, godiya yake da abun alkhairi. Ya biya shi, ya biya shi kudin. Hisbah aikin Allah."

kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu

Sai dai hakan bai yiwa mutane da dama a shafin na soshiyal midiya dadi ba, inda yawancinsu suke kallon hakan a matsayin ba daidai ba.

ummufaiz_collections ta yi martani:

“Ko a musulinci baa ce kayi aski kwal haka ba, gaskiya abun nasu yakamata a duba.”

offcl_mukhtar_tsy ya yi martani:

“Shin a Afghanistan muke.”

bg_designzstudio ya ce:

“Ko shakka babu an yiwa wani amfani da wannan abun askin kuma za a sake amfani da shi. Shin suna tsaftace shi?”

Kara karanta wannan

Saura kiris: Muna ta kokarin kawo karshen yajin aikin ASUU, inji gwamnatin Buhari

garba589 ya yi martani:

“Hakan ba daidai bane a dukkan matakai.”

sirdiq_a_salama ya ce:

“Wai godiya yake ”

Bayan aure da shekara 20, ya gane jikarsa ce, yace ba zai taba sakinta ba

A wani labarin, mun ji cewa wani magidanci mai shekaru 47, Alhaji Musa Tsafe a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara ya ki sakin jikarsa wacce ya aura tsawon shekaru 20 da suka wuce.

Ya ki yarda ya rabu da ita bayan an sanar dashi haramcin da ke tattare da irin wannan aure, jaridar Daily Trust ta rahoto.

An tattaro cewa matar mai shekaru 35, Wasila Isah Tsafe, ta haifi yara takwas a tsawon aurensu na shekaru 20.

Asali: Legit.ng

Online view pixel