‘Shugaban majalisar dattawa, kalle ni mana’, Buhari ya zolayi Lawan a cikin wani bidiyo

‘Shugaban majalisar dattawa, kalle ni mana’, Buhari ya zolayi Lawan a cikin wani bidiyo

  • Idan aka zo kan batun iya barkwanci, ba za a taba barin shugaban kasa Muhammadu Buhari a baya ba
  • Shugaba Buhari ya zolayi shugaban majalisar dattawa, Lawan Ahmad a wajen taron kaddamar da sabon kamfanin NNPC
  • Shugaban Najeriyan ya bukaci Lawan wanda hankalinsa ke wani waje daban da ya jiyo ya kalle shi a yayin da ya hau munbari don yin jawabinsa

Abuja - An yi yar karamar dirama a wajen kaddamar da sabon kamfanin man fetur na Najeriya da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a yau Talata, 19 ga watan Yuli.

Kamar yadda yake a wani bidiyo da jaridar Vanguard ta fitar, an gano Shugaban kasar cike da barkwanci yana zolayar shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, inda ya bukace shi da ya juyo ya kalle shi.

Kara karanta wannan

Babu sauran matsalar mai: Shugaba Buhari ya kaddamar da sabon kamfanin man fetur na NNPC

Taron wanda ya gudana a fadar shugaban kasa da ke Abuja ya samu halartan wasu manyan jami’an gwamnati.

Buhari da Lawan
‘Shugaban majalisar dattawa, kalle ni mana’, Buhari ya zolayi Lawan a cikin wani bidiyo Hoto: The Guardian
Asali: UGC

A lokacin da shugaban kasar ya hau munbari, sai aka yi masa maraba da zuwa. Sai dai kuma kamar wani abu ya janye hankalin Lawan daga gare shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Don haka, sai shugaban kasar wanda ke kan munbari don yin jawabinsa ya kalli inda Lawan yake sannan ya ce:

“Shugaban majalisar dattawa, ka kalle ni mana.”

Hakan ya baiwa wadanda suke wajen da shi kansa shugaban kasar dariya, yayin da shugaban majalisar dattawan ya yi mubaya’a ga Buhari sannan ya zaune kan kujerarsa.

Kalli bidiyon a kasa:

Babu sauran matsalar mai: Shugaba Buhari ya kaddamar da sabon kamfanin man fetur na NNPC

Mun kawo a baya mun kawo cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) a ranar Talata, 19 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Buhari Ga Yan Najeriya: Idan Da Kun San Wahalar Da Ake Sha A Wasu Kasashe Da Kun Gode Wa Allah

A wajen taron da aka gudanar a fadar shugaban kasa da ke Abuja, shugaban kasar ya kuma kaddamar da sabon tambarin NNPC.

Da yake jawabi, Buhari ya ce kamfanin man na kasa mafi girma a Afrika zai kuma taimaka wajen tabbatar da ci gaba mai dorewa a tattalin arzikin kasar yayin da yake samar da makamashi ga duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng