Manyan Labarai A Yau
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya yi shaguɓe ga Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP kan yawan zuwan da yake yi Villa wajen Tinubu.
Wani magidanci ya koka kan yadda matarsa da suka shekara shida suna zaman aure ta tafi ta bar shi bayan ya samu hatsari. Har ta ƴaƴansa sai da ta kwashe su.
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya yi zargin cewa gwamnatin jihar Zamfara ta tafka masa sata a gidajensa wajen ƙwato motocin da tace ya sace.
Dakarun sojin saman Najeriya sun samu nasarar kai mummunan farmaki kan maɓoyar ƴan ta'addan Boko Haram a jihar Borno, sun halaka ƴan ta'adda masu yawa a harin.
Tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya bayyana cewa shugaba Tinubu ba zai manta da El-Rufai ba. Umahi ya ce El-Rufai zai taka rawa sosai a mulkin Tinubu.
Mummunar gobara ta tashi a babbar kasuwar Bayan-Tasha a cikin birnin Damaturu na jihar Yobe. Gobarar ta laƙume kayayyakin ƴan kasuwa da dama na miliyoyin naira.
An gayyaci Rabiu Kwankwaso zuwa Aso Villa a kan rushe-rushen da ake yi, Kwankwaso ya fadawa Bola Tinubu Abdullahi Ganduje ya rika kwashe filayen talakawan Kano
Yar shekaru 13 ta kashe gaba daya kudaden da iyayenta suka tara a intanet kuma malamarta ta gano hakan. Mahaifiyarta na kokarin ganin an dawo mata da kudadenta.
Gwamnatin jihar Kano tana sanar da dukkanin masu kaya a shagunan da aka gina a filayen da wajajen da Ganduje ya siyar da su gaggawar kwashe dukkanin kayan su.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari