Gwamnatin Kano Za Ta Cigaba da Rushe-Rushe Bayan Rade-Radin Tilasta Dakatarwa

Gwamnatin Kano Za Ta Cigaba da Rushe-Rushe Bayan Rade-Radin Tilasta Dakatarwa

  • Sanarwa ta fito daga Gwamnatin Jihar Kano cewa masu dukiya a wuraren da za a ruguje, su cire dukiyoyinsu
  • Da alama za a ruguza gidaje, shaguna da ginin da su ke masallatai, makarantu, makabartu da wasu asibitoci
  • Sakataren Gwamnatin Kano, Dr. Abdullahi Baffa Bichi, ya fitar da sanarwar a madadin Mai girma Gwamna

Kano - Gwamnatin jihar Kano ta ja-kunnen al’umma a yunkurin da ta ke cigaba da yi na ganin an dawo da tsarin taswira da ta ke zargin an saba.

Rahoto ya zo daga gidan rediyon Freedom cewa Abba Kabir Yusuf ya bukaci duk wadanda su ke da kaya a inda za a rusa, su dauke dukiyoyinsu.

Mai girma Abba Kabir Yusuf ya gargadi wadanda suke gini a filayen al’umma kamar makabartu da wuraren ibada da su gaggauta tattara kayansu.

Kara karanta wannan

Ga irinta nan: Yadda aka yiwa masu kwacen waya 2 a Kano hukunci mai tsanani a kotun Muslunci

Gwamnatin Kano
Gwamnan Kano, Abba Gida Gida a Mariri Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Sauran wuraren da sanarwar ta yi magana a kai sun hada da asibitoci, jikin ganuwa, filayen ma’aikatu da wuraren shakatawa da wuraren wasanni.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnatin Abba Yusuf ta ce masu kaya a shaguna ko wasu gine-gine a wadannan wurare da asali gwamnati ta mallaka, su kaucewa yin biyu-babu.

A dauke kaya da gaggawa

Kamar yadda rahoton ya nuna sanarwar ta ce a dauke kayan ne ba tare da bata lokaci ba, amma ba a fadi takamaimen ranar da za a rusa gine-ginen ba.

Legit.ng Hausa ta fahimci Sakataren gwamnatin jihar Kano, Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya fitar da sanarwar a madadin gwamna a yammacin Alhamis.

Kafin nan wata majiya ta nuna gwamnatin Kano za ta cigaba da ruguza gidaje, shaguna da sauran gine-ginen da ake zargin an yi su ba a ka’ida ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Ƙara Albashi, Ya Rage Ranakun Zuwa Aiki Saboda Tashin Kudin Man Fetur

Mutane sun ci ganima

Ganin mutane su na kukan asara duk lokacin da aka yi rushe-rushen musamman cikin dare, shiyasa wannan karo aka ja-kunnen al’umma tun wuri.

Idan hukuma ta rusa wadannan gini cikin dare, zuwa safiya sai a ji bata-gari sun shiga wuraren su na satar kayan jama’a da sunan an samu ganima.

A jiyan ne mu ka ji sabon Gwamnan ya ziyarci makarantar mata da ke Mariri, sannan ya duba lafiyar motocin da za a rika kai yara zuwa karatu.

An kai karar Gwamnati a kotu

A farkon makon nan an ji labari kamfanin Lamash Property Limited ya bukaci Gwamnatin Abba ta biya sa N10bn domin rage zafin rusa Daula otel.

Shi kuma dan kasuwar nan, Alhaji ‘Dan Asabe Abubakar ya ce an jawo masa asarar Naira biliyan 1.4 a sakamakon rusa filin sukuwa da aka yi cikin dare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel