"Ta Kwashe 'Ya'yana Ta Tafi Da Su": Magidanci Ya Koka Bayan Matarsa Da Suka Dade Ta Rabu Da Shi

"Ta Kwashe 'Ya'yana Ta Tafi Da Su": Magidanci Ya Koka Bayan Matarsa Da Suka Dade Ta Rabu Da Shi

  • Cosmas Otwori Julius ya buɗe ido ya ganshi kwance a gadon asibiti bayan wani mummunan hatsari da da ya auku da shi
  • A lokacin da yake kwance a gadon asibiti, magidancin ɗan ƙasar Kenya ya rasa aikin kamfanin da yake yi bayan sun kore shi
  • Wata biyu bayan aukuwar hakan, matarsa wacce suka kwashe shekara shida tare, ta tattara komai na gidansa ta tafi ta bar shi

Wani magidanci ya bayyana labarinsa mai sosa zuciya bayan mummunan hatsarin da ya auku da shi a shekarar 2018 wanda ya sauya masa rayuwa.

Ɗan kasuwar ya bayyana cewa nan da nan rayuwarsa ta yi juyawar waina, inda ya koma baya da wani abin yi ba tare da wani wanda zai taimaka masa ba.

Magidanci ya koka bayan matarsa ta rabu da shi
Cosmos ya ce ya rasa komai bayan hatsarin Hoto: TUCO.co.ke/Shiru Mbugua
Asali: Original

Kuskuren fahimta aka samu a tsakanin direbobin

Kara karanta wannan

Matashiya Ta Bayyana Yadda Aurensu Da Tsohon Mijinta Ya Mutu Cikin Watanni 7 Kacal

Cosmas Otwori Julius ya bayyana cewa ya fito daga wajen wani taro da yammaci lokacin da hatsarin ya auku.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bayyana wa tashar TUCO.co.ke cewa saɓani aka samu a tsakanin direbobin wanda hakan ya haddasa hatsarin.

"Abinda kawai zan iya tunawa shi ne na tashi na ganni a gadon asibiti cikin matsanancin ciwo. Ƙafata ta karye ta yi min nauyi kamar an ɗora min itace akai. Wuya ne har gocewa ya yi."

"Bayan wata ɗaya, idona ya samu matsala inda na koma ina ganin duhu-duhu."

Matarsa ta guje shi bayan hatsarin

Bayan wata biyu matarsa wacce suka kwashe shekara shida tare, ta tattara dukkanin kayan dake gidansa tare da ƴaƴansa biyu ta tafi da su."

Otwori ya bayyana cewa ya rasa matarsa, idonsa, aikinsa da abokansa a cikin sati shida kacal da aukuwar hatsarin, wanda hakan ya sanya shi cikin baƙin ciki.

Kara karanta wannan

"Ba Wayau": Kyakkyawar Budurwa Ta Damfari Wani Matashi Da Ya Ce Yana Sonta, Ta Bar Shi Da Cizon Yatsa

Bidiyon Ango Na Sharɓar Kuka a Wajen Ɗaurin Aurensa Ya Ɗauki Hankula

A wani labarin na daban kuma, wani ango ya zo da sabon salo ranar ɗaurin aurensa inda ya zo da abin ban mamaki wanda ya ɗauki hankula sosai.

Angon dai kamar ƙaramin yaro ya saki baki sai sharɓar yake ta yi bayan ya hango amryarsa lokacin da ta shigo inda za a ɗaura musu aure su zama miji da mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel