Wane Mutum: Kwankwaso Ya Mayar Da Martani Mai Zafi Kan Barazanar Marin Da Ganduje Ya Yi Masa

Wane Mutum: Kwankwaso Ya Mayar Da Martani Mai Zafi Kan Barazanar Marin Da Ganduje Ya Yi Masa

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya mayar da martani kan barazanar marin da Ganduje ya yi masa
  • Kwankwaso ya ce Ganduje ko ƙwayar idonsa ba iya kallo idan suka haɗu ballantana har ya kai ga sa hannu ya mare shi
  • Tsohon gwamnan ya bayyana cewa lokacin da Ganduje ya yi wannan katoɓarar a ruɗe yake shiyasa ya yi wannan suɓutar bakin

Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi martana kan barazanar sharara masa mari da tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi.

Jaridar Aminiya ta kawo rahoto cewa Kwankwaso ya bayyana cewa Ganduje ko kallon ƙwayar idonsa ba zai iya yi ba, ballantana har ta kai ga ya zabga masa mari.

Kwankwaso ya yi martani kan barazanar marinsa da Ganduje ya yi
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Aminiya.com
Asali: UGC

Kwankwaso ya bayyana cewa Ganduje a ruɗe yake lokacin da ya yi barazanar sharara masa mari a fadar shugaban ƙasa, bayan ya kai ƙarar gwamnan da ya ƙarbi mulki a hannunsa, Abba Gida-Gida a gaban shugaba Tinubu.

Ganduje ya kai ƙarar gwamnan na jihar Kano ne a gaban Tinubu bisa rusau ɗin da gwamnan yake ta yi a filayen da gwamnatinsa ta yi gine-gine ko ta siyar da su a kasuwa a jihar, cewar rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya yi martani kan barazanar marin da Ganduje ya yi masa

A martanin da Kwankwaso ya yi kan batun marinsa da Ganduje zai yi, ya ce Gandujen a ruɗe yake lokacin da ya yi wannan suɓutar bakin.

Ya bayyana cewa irinsu Ganduje yaransa ne a siyansance waɗanda ko haɗa ido da shi ba sa iya yi idan mai haɗawa ta haɗa su.

"Na ji cewa (Ganduje) ya ce zai mare ni, to ai ga ni nan. Ya ruɗe ne kawai." A cewarsa.
“Waɗannan duk yarana ne a siyasance, ba sa iya kallona kai-tsaye idan muka hadu."

"A gigice yake a lokacin da ya fadi haka, amma dukkansu yarana ne ’yan siyasa wadanda idan sun gan ni sunkuyar da kansu suke yi."

Kwankwaso Ya Fadi Abin da Ya Shaidawa Tinubu Kan Ganduje

A wani rahoton na daban kuma, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana yadda ta kasance a tsakaninsa da Shugaba Tinubu bayan sun sanya labule.

Kwankwaso ya ce Tinubu ya yi matuƙar mamakin irin taɓargazar da Ganduje ya riƙa tafkawa akan kujerar mulkin Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel