Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, Ya Yi Wa Atiku Abubakar Shagube

Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, Ya Yi Wa Atiku Abubakar Shagube

  • Gwamnan jihar Oyo, ya yi wa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, shaguɓe a bainar jama'a
  • Seyi Makinde ya ce a maimakon zuwa Yola zai ci gaba da zuwa Abuja domin neman dawo da kuɗin da ya kashe wajen yin hanyoyi
  • Gwamnan yana daga cikin gwamnonin PDP masu takun saƙa da ɗan takarar shugaban ƙasan na jam'iyyar PDP

Jihar Oyo - Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, ya yi shuguɓe ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar.

Makinde yana ɗaya daga cikin gwamnonin da suka juyawa Atiku baya a lokacin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, lokacin suna cikin ganiyar ƙungiyarsu ta G5.

Makinde ya yi wa Atiku shagube
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde Hoto: Leadership.com
Asali: UGC

Sai dai, tun bayan da aka kammala zaɓen shugaban ƙasa sannan aka rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban ƙasa, an sha ganin Seyi Makinde a fadar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojin Sama Sun Yi Luguden Kan Maboyar 'Yan Boko Haram a Borno, Sun Sheke Manyan Kwamandoji Da Yawa

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa gwamna Makinde ya kare yawan ganinsa da ake yi a fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock Villa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Makinde ya ce ba zai daina zuwa Villa ba

Gwamnan ya kare kansa ne yayin da yake ƙaddamar da aikin faɗaɗa titin hanyar 8.3 kilometer Akobo-Olorunda mai tsawon kilomita 8.3 a jihar Oyo, cewar rahoton Daily Post.

"A yayin da na ke zuwa Abuja domin ganawa da shugaban ƙasa, na san cewa wasu mutanen suna ta tsegumi cewa tunda aka rantsar da shugaban ƙasa, na je Aso Rock wajen sau huɗu a cikin sati ɗaya." A cewarsa
"Ina kuke son na je to? Shin Yola kuke so na je? Ni ba ruwana zan ci gaba da zuwa inda za su iya dawo mana da kuɗin da mu ka kashe wajen gina titin hanyoyin gwamnatin tarayya. Saboda haka zan ci gaba da zuwa Aso Rock domin roƙon a dawo mana da kuɗin."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: INEC Ta Saki Jerin Sunayen 'Yan Takarar Gwamna a Jihohin Kogi, Bayelsa Da Imo

Duk da cewa gwamna Makinde, bai bayyana sunan Atiku ba kai tsaye, alamu masu ƙarfi sun nuna cewa kalaman nasa ya yi su ne akan tsohon mataimakin shugaban ƙasar.

Gwamna Fubara Ya Gana Da 'Yan Majalisa

A wani labarin, gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya gana da zaɓaɓɓun ƴan majalisa da sanatocin da suka fito daga jihar Rivers.

Gwamnan ya umarci sanatocin da ƴan majalisar wakilan da su zaɓi ƴan takarar da jam'iyyar APC ta tsayar a kujerar shugabancin majalisar dattawa da ta wakilai.

APC ta ayyana Sanata Godswill Akpabio a matsayin zaɓinta a shugabancin majalisar dattawa, yayin da ta zaɓi Abbas Tajudeen a matsayin wanda zai shugabanci majalisar wakilai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel