Dave Umahi Ya Bayyana Rawar Da El-Rufai Zai Taka a Gwamnatin Shugaba Tinubu

Dave Umahi Ya Bayyana Rawar Da El-Rufai Zai Taka a Gwamnatin Shugaba Tinubu

  • Tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Dave Nweze Umahi, ya bayyana muhimmiyar rawa da El-Rufai zai taka a mulkin Tinubu
  • Umahi ya bayyana cewa Shugaba Tinubu zai sakawa mutane irinsu El-Rufai saboda ƙoƙarin da suka yi masa a lokacin zaɓe
  • Tsohon gwamnan ya ce Tinubu mai mayar da biki ne hakan ya sanya zai dama da El-Rufai da sauran waɗanda suka taimaka masa lokacin zaɓe

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai zai taka muhimmiyar rawa a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Jaridar The Cable ta ambato Umahi na bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da gidan talbijin na Arise tv.

Dave Umahi ya bayyana rawar da El-Rufai zai taka a mulkin Tinubu
Tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi Hoto: Premiumtimes.com
Asali: UGC

A yayin tattaunawar an buƙaci jin ta bakin tsohon gwamnan kan cewa ko Shugaba Tinubu zai nesanta kansa da El-Rufai, wanda wani bidiyonsa ya fito inda ya ke cika bakin cewa musulmai ne za su ci gaba da jan ragamar ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Wike Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Kan Matakin da Shugaba Tinubu Ya Ɗauka Na Dakatar da Gwamnan CBN

Umahi wanda zaɓaɓɓen sanata ne na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ba zai nesanta kansa daga mutanen da suka tsaya tsayin daka wajen ganin ya samu nasara a zaɓe ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wace irin rawa El-Rufai zai taka a gwamnatin Tinubu?

Ya bayyana cewa El-Rufai zai taka muhimmiyar rawa a gwamnatin Tinubu saboda shugaba Tinubu yana saka alkhairi da alkhairi.

A kalamansa:

"Shugaban ƙasa bai nesanta kansa da mutanen da suka yi masa aiki ba. Dukkanin mutanen nan da suka yi masa aiki suna da hurumin ganin shi kai tsaye."
"Ina tabbatar mu ku Shugaba Tinubu ba zai ƙyale mutane irinsu El-Rufai ba da sauran ire-iren mu da muka yi masa aiki kai da fata."
"Tarihinsa a bayyana ne ya ke. Ba ya yaudarar kowa. Domin haka ina da tabbacin cewa abokina El-Rufai zai taka muhimmiyar rawa."

Kara karanta wannan

"Ba Daina Zuwa Wurin Shugaba Tinubu Ba Saboda Abu 1" Gwamnan PDP da Yaje Villa Sau 4 a Sati Ya Faɗi Dalili

"Ba ina magana bane da yawun shugaban ƙasa, amma ina magana ne saboda halayyarsa wacce na sani sosai."

El-Rufai Ya Fadi Dalilinsa Na Goyon Bayan Tinubu

A wani labarin na daban kuma, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai, ya bayyana dalilin da ya sanya ya tsaya kai da fata sai Tinubu ya zama shugaban ƙasa.

Eƙ-Rufai ya ce ya goyi bayan Shugaba Tinubu ne saboda Musulmai ƴan yankin Kudu maso Yamma su fito a riƙa damawa da su a harkokin mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel