Shugaba Tinubu Bai Dakatar Da Mele Kyari Daga Shugabancin NNPCL Ba

Shugaba Tinubu Bai Dakatar Da Mele Kyari Daga Shugabancin NNPCL Ba

  • Saɓanin rahotannin da ke ta yawo a kafafen sada zumunta, shugaba Tinubu bai dakatar da Mele Kyari daga muƙamin shugaban NNPCL ba
  • Labaran dakatar da Kyari sun karaɗe shafukan sada zumunta ne biyo bayan dakatar da gwamnan CBN, Godwin Emefiele
  • Sai dai, majiyoyi masu ƙarfi daga fadar shugaban ƙasa sun tabbatar da cewa ƙanzon kurege ne kawai labarin dakatar da Kyari

Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, bai dakatar da shugabann kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ba, Malam Mele Kyari, saɓanin rahotannin da ke ta yawo a soshiyal midiya.

Majiyoyi masu ƙarfi daga fadar shugaban ƙasa sun gayawa jaridar Tribune a daren ranar Asabar cewa, shugaban ƙasar bai bayar da umarnin dakatar da Ƙyari a matsayin shugaban kamfanin NNPCL.

Shugaba Tinubu bai dakatar da Kyari ba
Malam Mele Kyari shugaban kamfanin NNPCL Hoto: Leadership.com
Asali: UGC

Kafafen sada zumunta dai sun ɗauki ɗumi a yammacin ranar Asabar da labarin cewa shugaban ƙasa ya dakatar da Kyari daga shugabancin kamfanin NNPCL.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Mayar Da Atiku Abin Tsokana, Ya Yi Masa Shagube a Bainar Jama'a

Labaran sun yaɗu ne saboda sun zo ne ƙasa da sa'o'i 24 bayan fadar shugaban ƙasa ta sanar da dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba a dakatar da Mele Kyari ba daga muƙaminsa

Majiyoyi da dama daga fadar shugaban ƙasan sun bayyana cewa babu wani shirin dakatar da Kyari daga muƙaminsa, cewar rahoton Vanguard.

Ɗaya daga cikin majiyoyin ya bayyana. cewa:

"Mu ma a soshiyal midiya mu ka ga labarin dakatarwar. Amma ina tabbatar mu ku da cewa babu wannnan umarnin daga shugaban ƙasa. Ƴan Najeriya sun ƙware wajen son abinda zai yi ta yawo, sannan wani kawai na iya zama ya tsara wannan labarin."
"Babu ƙanshin gaskiya ko kaɗan a wannan wallafar da aka yi mai cewa shugaban ƙasa ya dakatar da Kyari. Babu wani abin ɗaga hankali akai saboda kundin doka ya yi bayanin yadda za a iya cire shugaban NNPCL ko wani mamba na kamfanin."

Kara karanta wannan

"Bai Kamata Tinubu Ya Iya Dakatar Da Emefiele Ba": Fitaccen Lauya Ya Bayyana

Wani hadimin sakataren gwamnatin tarayya ya yi nuni da cewa ofishinsu bai samu wannan umarnin ba daga wajen shugaban ƙasa.

DSS Za Ta Bukaci Cigaba Da Tsare Emefiele

A wani labarin, kun ji cewa hukumar DSS za ta garzaya kotu domin neman iznin ci gaba da tsare dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Hukumsr za ta buƙaci hakan ne domin samun cikakken lokacin da za ta yi bincike kan zarge-zargen da ake yi wa Emefiele.

Asali: Legit.ng

Online view pixel