Yar Shekaru 13 Ta Kashe Miliyan N40 Da Iyayenta Suka Tara Wajen Buga Wasanni Ta Intanet

Yar Shekaru 13 Ta Kashe Miliyan N40 Da Iyayenta Suka Tara Wajen Buga Wasanni Ta Intanet

  • An rahoto cewa wata matashiya ta kashe naira miliyan 40 na iyayenta wajen buga wasanni a intanet
  • Uwa ta gano hakan bayan malamar diyarta ta ja hankalinta kan yawan buga wasanni da diyar tata ke yi sannan ta duba asusun bankinta
  • Yarinyar ta yarda cewa ta sace katin bankin da lambobin sirri sannan ta goge bayanan biyan kudi

Wata matashiya yar shekaru 13 daga Henan, kasar China, ta jefa iyayenta cikin kaduwa bayan sun gano cewa ta kashe kimanin naira miliyan 40 na kudadensu a wajen buga wasanni ta waya cikin watanni hudu kacal.

Yarinyar ta sace katin bankin mahaifiyarta da lambobin sirri sannan ta yi amfani da shi wajen siyan wasanni da manhajoji.

Yara na buga wasanni
Yar Shekaru 13 Ta Kashe Miliyan N40 Da Iyayenta Suka Tara Wajen Buga Wasanni Ta Intanet Hoto: Dexerto
Asali: UGC

Matashiya ta dabi'antu da buga wasanni a waya

Ta kan kuma ba abokan karatunta da ke son buga wasanni kudi suma su siya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Malamar makarantar yarinyar ce ta fallasa dabi'arta na son buga wasanni a waya, bayan ta gano yadda take kashe lokacinta a kan wayarta sannan ta tuntubi mahaifiyarta.

Mahaifiyar ta duba asusun bankinta sai ta gano cewa yan silalla kadan ne suka yi mata saura.

Ta tunkari diyar tata wacce ta yarda cewa ta kashe kudaden ne a kan wasanni.

Yarinyar ta ce bata san wani abu sosai game da kudaden ko daga inda suke fitowa ba. Ta ce bata jin baiwa abokan karatunta kudi, amma sai su dame ta idan ta ki.

Ta kuma ce tana jin tsoron sanar da malamarta ko iyayenta game da dabi'arta na buga wasanni.

Don boye kashe-kashen kudin da take yi, ta kan goge duk wasu bayanai da biyan kudin da ta yi daga wayarta.

Mahaifiyar yarinyar ta yi kokarin ganin kamfanonin da aka biya wa kudi sun dawo mata da kudadenta, amma bata samu cikakken kudin ba tukuna. Ta ce abin da ‘yarta ta aikata ya bata mata rai, kuma tana fatan sauran iyaye za su yi koyi darasi daga kuskuren ta.

Samu ainahin labarin a nan.

Matashi ya samu sha-tara ta arziki bayan ya yi wa wata matashiya kyautar piya wata daya

A wani labari na daban, wata mata ta yi wa wani matashi mai sana'ar piya wata sha-tara ta arziki bayan ya yi mata kyautar ruwa leda daya.

Matashiyar ta roki matashin cewa ya bata ruwa tana jin kishirwa amma bata da kudi nan take ya mika mata, sai ta ba shi katan-katan na lemuka don ya kara jari.'

Asali: Legit.ng

Online view pixel